Sharidu da Matakai bakwai 7 ga zaben 2019 – Hukumar INEC

Hukumar Kadamar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta bayyana matakai bakwai da za a bi wajen jefa kuri’u a ranar zabe ta 2019

Hukumar sun gabatar da wannan ne a ranar Alhamis 10 ga Watan Janairu, 2019.

Sharidu da Matakai bakwan 7 na kamar haka:

Matakin Farko 1:

Idan ka ko kin halarci wajen jefa zaben sai a shiga layi yayin da daya daga cikin mallaman zabe (APO111) zai duba, ya kuma tabbata da cewa lallai wajen ne gidan zaben ka, ya kuma duba hoton da ke a katin ka ko lallai daya ne da fuskar sa’anan ya nuna maka waje na gaba, watau wajen (APO1).

Mataki na Biyu 2:

Shi (APO1) zai karbi katin zaben ka ya yi bincike don tabbatar da cewa lallai katin naka ne, zai kuma gwada shi da na’urar duba katin zabe don tabbatar da hakan, za a binciki hoto, suna, a kuma gwada yatsun ka ko sun dace da wanda ke akan na’urar.

Mataki na Uku 3:

Shi wannan Malamin zaben zai (APO11) zai karbin katin zaben ka ya duba ko daidai ne abubuwan da ke akai da wanda ke rubuce a takardar sa, idan har dadai ne sai ya rattaba hannun ga takardar da alamun cewa lallai komai na dadai sa’anan ya diga alli ga yasan ka don bada alama chewa an yi maka bincike ta gaske kuma ka na a shirye don jefa zabe.

Mataki na Hudu 4:

Shi kuma wannan Malamin zaben (PO) zai buga hatimi ga takardar zaben ga ya kuma rattaba hannu da sa rana da shekara da ya yi wannan sa hannun don shaida. Malamin zai nada takardar ya kuwa mika maka shi ta ciki sa,anan ya gwada maka inda zaka je ka jefa kuri’ar ka inda babu wanda zai gani ko ya nuna maka wani abu.

Mataki na Biyar 5:

Bayan Malamin ya yi wannan, sai ka rattaba yatsan ka ga allin zaben da aka aje wajen zaben, sa’anan sai ka danna yatsan ga inda dan takaran ka da kake so ya ke ba tare da ka bata takardan ba sai ka sake nada takardar kaman yadda malamin zaben ya mika maka, yadda babu wanda zai hangi zabin ka.

Mataki na Shidda 6:

Bayan ka bi wadanan sharidun, sai ka kara gaba ga jefa kuri’ar ka cikin akwatin zabe kowa na ganin hakan.

Mataki na Bakwai 7:

Idan har ka gama jefa kuri’ar ka, an bukaci ka bar wurin ka wuce abinka. Amma idan har ka so ka tsaya har ga karshe don jin sakamakon zaben wajen, an bukaci kuwa ka koma gefe ba tare da wata fitina ko tashin hankali ba har a gama zaben.

Duba: Babban Malamin zaben zai manna sakamakon zaben a bango don kowa ya gani bayan an kare gudanar da zaben ranar.

 

Karanta kuma: Zamu gudanar da zaben 2019 a hanyar doka – in ji Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar zabe ta kasa (INEC)