Connect with us

Labaran Nishadi

Bukola Saraki: An kai farmaki giman gadon Sanata Bukola Saraki da ke Jihar Kwara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Da ‘yan kwanaki kadan da zaben tarayya  da ke gaba a ranar 16 ga Watan Fabairu, 2019. ‘Yan ta’addan siyasa na ta kai wa juna farmaki ko ta ina a kasar.

Naija News Hausa ta sami rahoto da baya da cewa an kai hari a Ofishin dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ofishin sa da ke a garin Akure, Jihar Ondo sati da ta gabata har ma ‘yan ta’addan sun kwace wayar mai gadin, suka kuma daure shi bayan sun anshe masa wayoyin sa.

Duk, da hakan Farmaki ba ta tsaya nan ba.

Naija News ta samu rahoto da cewa ‘yan ta’adda sun kai farmaki a gidan gadon babban shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki satin da ta gabata.

Mun sami cikakken labari da cewar farmakin ya faru ne a wata anguwa da suna Agbaji, anan cikin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, inda gidan gadon babban sanatan yake.

Sanatan ya bayyana bacin ran sa da wannan mugun harin, kuma ya iya bayyana da cewa ‘yan Jam’iyyar APC ne suka aikata wannan kuma ya zargin Jami’an ‘Yan sanda da taimakawa wajen aiwatar da farmakin.

Ya ce, “Yan Sandan su kare ‘yan ta’addan ne har suka sami shiga gidan gadon mu da ke Agbaji, Ilorin inda suka lallata motoci, gidaje, shaguna kuma suka yi wa mazaunin wajen raunuka da dama”.

”Duk wannan barnan ya faru ne a gaban ‘yan sanda amma ba su iya yin komai ba saboda sun zo ne tare da su, kuma suka bar ‘yan Jam’iyyar APC da yan tada hankalin zaune har suka aiwata wannan halin kaiton.

“A kashin gaskiya wannan farmakin da aka kai a gidan gadonmu ya nuna da cewa rai na ake bida da dauke wa”

“Duk wata mafara ko alamu da ‘yan Jam’iyyar APC da ‘yan tada hankali zaunen su ke da shi kuma suke aikata wa, ni a gareni matakin banza ne kuma halin rashin wayo da kuma rashin hankali ne” in ji Saraki.

Bolarinwa Bashir, shugaban Jam’iyyar APC na Jihar ya bayyana da cewa ‘yan tada hankali zaunen da suka aiwatar da wannan magoyan baya ne na Jam’iyyar APC.

Ya ce, “sun fara ne da jifan duwatsu kamin nan suka karu da yawa har suka aikata mugun harin” in ji Bashir.

Kali bidiyon a nan kasa wanda aka samu daga wani da ya aika a yanar gizon nishadi ta facebook;

https://www.facebook.com/123838944328164/videos/211096883060071/

 

Karanta kuma: Farmaki ya tashi tsakanin mazaunin Jihar Kogi biyu, watau yaren Egbira da Bassa-Kwomu.