Connect with us

Uncategorized

Farmaki: An kashe mutane Uku, wasu kuma sun yi raunuka a yankin Jema, Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An sami rahoto da cewa wasu ‘yan hari da ba a san dasu ba, sun fada wa yankin Jema dake Jihar Kaduna

Wannan harin ya faru ne kamar yadda muka sami rahoto a ranar Asabar da ta gabata, a misalin karfe 7:30 na yamma.

Farmakin ya faru ne tsakankanin gadan Asso da Tanda a wani kauyen Gwong da ke yankin Jema’a, Jihar Kaduna.

Ciyaman na yankin, Mista Peter Averik ya tabbatas da farmakin ga manema labarai a yau, Mista Peter ya ce “Harin ya abku ne daidai misalin karfe 7:30 na maraice a yayin da maharan suka fado wa mazaunan kauyen da ke akan tafiyarsu tsakanin gadan Asso da gadan Tanda.

“An gaya mani ne cewa maharan sun harbi mutanen ne da tsoron kada su tona su a yayin da suka hange su” in ji Mista Peter.

“Mutum guda ya mutu a nan wajen, biyun kuma an kai su a asibitin da ke Fadan Kagoma inda ake nuna masu kulawa, a nan kuwa asibitin ne guda kuma ya mutu sanadiyar raunuka da ya samu” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Wasu yan hari sun kai farmaki har sun kashe mutane 14, sun kuma yiwa mutane 17 rauni a wata kauye mai suna Ungwan Paa-Gwandara a yankin Jema’a na Jihar Kaduna.

Mista Peter Averik ya kara da cewa na ukun ya mutu ne da safiyar Litini, watau a yau in da aka same shi bakin daji kwance ba rai a wata kauyen Wazo, kamin a kai kauyen Aso.

A halin yanzu an rigaya an yi shiri don kai wadanda suka sami raunuka a asibitin musanman ta Barau Diko, Jihar Kaduna, kamin dada akai su babban asibin Patrick da ke Kanfanchan.

Mista Peter ya karshe da cewa an riga an zuba jami’an tsaro a wajen da wannan farmakin ya abku don tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiyar mutanen yankin da tattalin arzikin su.

 

Karanta kuma: ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Habiba Usman da zargin cewa tana da sani kuma itace sanadiyar sace ta da barayi suka yi – in ji Yan Sanda.