Connect with us

Uncategorized

Jami’an ‘yan sanda sun yi karar Dino Melaye zuwa kotu da zargin ajiyar bindigogin da ba bisa doka ba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an ‘yan sanda sun cin ma bindigogin da ba bisa doka ba a gidan Sanata Dino Melaye

‘Yan sandan sun kai karar Sanata Dino Melaye a babban Kotun Tarayya da ke a birnin Abuja da zargin cewa sun cin ma manyan bindigogi a gidan Melaye a yayin da suke bin cike gidar a watan Yuli, shekarar 2018 da ta wuce a gidan sanatan da ke Jihar Kogi.

Naija News ta ruwaito da cewa a watan Disamba 2018 da ta gabata, Jami’an Yan Sandan Najeriya sun fada wa gidan Sanata Dino Melaye da ke birnin Abuja binciken neman kama shi, harma suka mamaye gidan har ga kwana 8 kamin ya mika kansa ga ‘yan sandan bayan kwanaki 8.

‘Yan Sanda sun kai karar Sanata Dino, Sanatan da ke wakiltar yammacin Jihar Kogi a babban gidan Majalisar Dinkin Duniya da zargin ajiyar bingigogi ba doka bata yadda da su ba a gidansa.

Naija News Hausa ta kara tuna da cewa a baya ta ruwaito da cewa Sanata Dino Melaye ya sunbude zai fadi a yayin da yan sanda ke batun shigar da shi a Ofishin jami’an DSS.

Bayan wannan sunbudewar Melaye, ‘Yan Sanda su yi masa kulawa a asibiti kuma sun bada tabbacin cewa yana da cikakken lafiya yanzun nan, kuma ana ina kai shi ga kara.

An zargin Melaye ne da laifuka shaidanci da kuma halin kisan kai tun 19 ga watan Yuli, shekarar 2018 da ta gabata.

Shaidu takwas, hade da ‘yan sanda shida da wasu maza biyu ne ke shirye a matsayin shaidu ga wannan zargin da ake wa Sanata Dino Melaye.

  • Rahoto ta bayar da cewa Mazan biyu an cin masu ne a gidan Sanatan suna yi wa gidan sa fenti a lokacin da ‘yan sanda suka hari gidan kwanakin baya da bincike.
  • ‘Yan Sandan da ke shaidar wannan zargin kuma na kamar haka:  DSP Babagana Bukar, DSP Ibrahim Abalaka, ASP Abdullahi Musa, Mataimakin Inspector Atabo Okpanachi, Inspector Apeh Peter, Theophilus Nuhu, Matthew Anthony da ASP Mohammed Onu.

Daya daga cikin mazaje biyun da aka cin ma a gidan Dino, mai suna Theophilus Nuhu ya ce “Babban Oga na, Mista Peter ne ya kawo ni da Mathew Anthony daga Jihar Kaduna zuwa Jihar Kogi don aikin fenti a gidan sanatan da ke Ayetoro, Gbede da ke a Jihar Kogi” in ji Nuhu.

” A yayin da muke cikin aikin mu ne Jami’an tsaro suka shigo gidan da bincike, suka kuwa cinma wata muguwar bindiga da alsasu a karkashin hure da ke anan kewayen gidan, ni kuwa ban san wanda ya ajiye bindiga ba“ in ji Theophilus Nuhu.

 

Karanta kuma: Rundunar Sojojin Najeriya sunyi barazanar cin nasarar yaki da ‘yan Boko Harama a garin Baga da ke Jihar Borno