Connect with us

Labaran Najeriya

Ka dakatar da karyanka game da Buhari – Shugabanci ta gayawa Gwmana Ortom

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugabancin kasar ta gargadi Gwamna Samuel Ortom, Gwamnar Jihar Benue da cewa ya dakatar fade-faden sa na karya game da shugaba Muhammadu Buhari a wajen shirin neman aikin siyasar sa.

Bugu da ƙari, A sanarwar shugabanci ta ranar Lahadi da ta wuce da aka bayar daga sa hannun Garba Shehu, Babban Mataimakin Shugaban kasa ta hanyar sadarwa, ya umurci jama’ar Jihar Benue cewa kada su yarda gwamnan ya yaudare su da maganganun karya da zargin karya akan Shugaba Buhari.

Sanarwar na kamar haka:

“Shugabanci ta umurci Gwamna Samuel Ortom, Gwamnan Jihar Benue don dakatar da ikirarin sa da fade-faden sa na yaƙin neman zaɓe har ga kafa baki ga karya game da Shugaba Muhammadu Buhari.”

“Tabbas, Gwamna Ortom ya kafa yakin neman zaben sa ne don jawo kiyayya da rashin amincewa a Jihar na irin bayyana wa al’umman Jihar Benue da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin mayar da Jihar kasar musulunci ne”

“An kuma gane da cewa Gwamnan na bin Ikklisiyu da ke Jihar don cika su da karya cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin zamar da Jihar Benue kasar musulummai” a kalamansa.

Ya kamata wannan mugun zargin ya dakata kuma ya bar hakan.

Naija News ta ruwaito da cewa Manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar sunyi yaba wa Shugaba Muhammadu da irin taimako ta musanman na yaki da ta’addacin Boko Haram a Jihar Borno”.

Ganin irin taimakawa da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya ta yi wa Gwamna Ortom da Jihar Benue, bai dace a ce shine ke aikata ko samar da irin wannan halin ba.

A sanarwar; Gwamnatin tarayya ta yi kira ga jama’ar Jihar da cewa su yi watsi da kowace irin karya da Gwamnan zai zo masu da ita. kuma su tuntube shi da dalilin da ya sa bai biya albashin ma’aikatan Jihar ba da kuma albashin tsofin ma’aikata da suka yi ritaya, duk da cewa akwai isasshen kudi a Jihar ta sanadiyar man fetur da ake bulbulawa a Jihar.

 

Karanta kuma: Ba zan gudanar da neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar – inji Buhari