Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini 14, ga Watan Janairu, a Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini 14 ga Watan Janairu, 2019

 

1. An sake gurfanar da Kwamishanan ‘Yan Sanda, Imohimi Edgal a Jihar Legas

An sake gurfanar da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, Imohimi Edgal. Kamfanin yada labarai ta Naija News ta bayar a baya da cewa an Imohimi yayi ritaya kuma an musanya gurbin sa da Fatai Owoseni wanda shi ma yayi ritaya a Watan Agusta, 2017 da ta gabata. An mayar da Imohim Edgaal zuwa hedkwatar ‘Yan Sanda ta birnin Abuja.

2. Takaitacen ganawa da Gwamnonin Kudu ta Kudu suka yi akan CJN

Gwamnonin Kudu maso Kudu kasar Najeriya sun umurci Walter Onnoghen Babban Alkalin Shari’ar Najeriya (CJN) da cewa yayi watsi da zartarwa ta Kotu.

Gwamnonin yankin biyar sunyi wata ganawa a birnin Abuja a ranar Lahadi da ta gabata inda suka zargi Shugaba Muhammadu Buhari da cewa shugaban bai nuna kulawa ta kwarai ba ga yankin Jihar Niger Delta.

3. Zan nemi mafita ga ‘ Apapa Gridlock’ tsakanin kwanaki 100 na a shugabanci – in ji Sanwo-Olu

Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Legas daga Jam’iyyar APC, Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi alkawari da barazanar cewa zai nemi mafita ga Apapa tsakanin kwanaki 100 na farko a mulkinsa idan har aka zabe shi kuma ya ci. Dan takarar ya bayyana wannan ne a ganawar gasar ‘yan takara da ake gudanar a Jihar.

4. Buhari da Jam’iyyar  APC na Shirin hasara ga zaben 2019 – inji Atiku

Dan takarar shugaban kasa ta jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce hukuncin da ake shirin yi wa babban alkali Walter Onnoghen, ya nuna da cewa Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa APC na shirin fadawarsu ga hasara ga zaben shugaban kasa na gaba. Wannan bayani ne da aka samu a ranar Asabar daga bakin  Phrank Shaibu, Mataimaki Harkokin Sadarwar Jam’iyyar PDP a wata zamar “Dimokradiyya a yau” da aka yi a yau wanda Naija News ta tabbatar da wannan.

5. Ayi bincike mai kyau kamin hukunta Alkali Onnoghen – inji Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Yakubu Dogara ya yi kira da cewa a yi la’akari da zargin da ake tuhumar babban Alkalin Shari’ar Najeriya, Walter Onnoghen. A wata sanarwar da aka bayar a ranar Lahadi, Hon Dogara ya ce yayin da hukumomi ke bincike akan wannan karar, ya dace abi hanyar da ta dace wajen  gudanar da shari’ar saboda Najeriya kasa ce mai dokuna ba kawai haka ta ke ba.

6. Na yaba maku, Kungiyar Manyan Jihar Borno – inji Atiku

Dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na yaba wa Kungiyar Manyan shugabanan Jihar Borno (Elders Forum) don sakon da suka aika wa shugaba Buhari na cewar ya kamata shugaban ya daina halin sake ‘yan ta’adda da aka kame don sun fada da cewa sun tuba, “wanan bai da ce ba” in ji Shugabanan Jihar.

Atiku ya ce “shekara da ta gabata, na bawa Buhari shawarar hakan harma sau biyu, amma bai amince da ni ba”

7. Kungiyar NANS ta yi kira ga Gwamnatin tarraya cika yarjejeniyar su da Hukumar ASUU

Ƙungiyar ‘Yan Jami’a ta Tarayya kasar Najeriya (NANS) sun yi kira ga gwamnatin tarayya da cewa su yi kokarin cika alkawurran da suka yi wa kungiyar Jami’o’i (ASUU) don tabbatar da gudanar da karatu a jami’o kasar.  Mista Bestman Okereafor Shugaban yada Labaru ga Kungiyar NANS ne ya gabatar da wannan a wata sanarwa da aka bayar a ranar Lahadi a Jihar Enugu.

8. Nnamdi Kanu yayi juyayi ga fadin sa, Ya ce IPOB zata yi zabe a Jihar Ebonyi da Jihar Abia

Shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce membobin kungiyar zasu shiga lamarin zaben Gwamnoni ta gaba a Jihar Abia da kuma Jihar Ebonyi. Kanu ya bayyana wannan ne a ranar Asabar a gidan radiyo Biafra. Naija News na da tabbacin ya fada cewa zasu tsige Gwamna Okezie Ikpeazu da Gwamna Dave Umahi da fadin cewa su biyun makiyar kungiyar Biafra ne.

9. Hukumar (NBA) da Sauran hukumomi Sun yi rashin amincewa da zargin Alkali Walter

Hukumar NBA da wasu Alkalai sun nuna rashin amincewa da shirin shari’a da ake batun yi wa babban Alkali Walter Onnoghen a yau, Litini 14 ga Watan Janairu a birnin Abuja.

Alkalin da ake zargin sa da wasu laifin gabatar da kasafi shidda wadda ba daidai ba ne.

10. An yi wa Maradona aikin Tiyata, kuma yana a dakace a Asibiti

Kwararren dan wasan kwallon kafan da na kasar Argentina, Diego Maradona ya samu nasara ga fidar da aka yi masa a ranar Asabar da ta wuce, kuma ya saura a nan asibitin Buenos Aires a inda aka yi masa aikin fidar.

“Tiyatan da aka yi wa Diego Maradona ya kasance da nasara, godiya ga Allah ga abin da ya faru” in ji Lauyan sa a yanar gizon twitter.

 

Sami cikakken labarai daga Naija News Hausa