Yan Ta’adda sun fada wa Ofishin Atiku dake Akure, Jihar Ondo

Wasu ‘yan ta’adda da ba iya gane su ba sun hari Ofishin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

‘Yan ta’addan da ake zargin su da yin barna da muzuntawa sun hari Ofishin ne da ke kusa da makarantan Jami’ar FECA da ke a hanyar Ijapo nan yankin Akure a Jihar Ondo, a ranar 10 ga Watan Janairu, 2019 da ta wuce, a yadda rahoto ta bayar. A samu bayani da cewa ‘yan ta’addan su fado wa gaban ofishin ne da wake-wake, suna kirarin (NEXT LEVEL) watau ‘GABA DAI‘.

An sami wannan bayani ne daga bakin mataimakin shugaban gudanarwar Jam’iyya da ke a Jihar, mai suna Olumide Ogunkua.

“Sun fado ne wa gaban ofishin da wake-wake da kirari, suna ta barnan kalandu da fostoci da aka manna da kuma wadanda aka kafa da ke dauke da hoton Atiku da Obi” in ji Maigadin ofishin a yayin da aka bukaceshi da bayani akan abin da ya faru.

Ya ce, “na yi kokarin kiran taimako a yayin da na hange su amma sai suka hau katanga, suka fado mani da bugu har ma sun karbi wayoyi na kuma suka daure ni sa’anan suka koma da yin barnan”.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, FPRO, Ag. DCP Jimoh MOSHOOD ya bada tabbacin cewa jami’an za su yi iya kokarin su da ganin cewa babu wata matsala ga Zaben 2019 da ke gaba.

In ji Ogunkua, “bayan mun samu kira daga wasu masoyan mu, sai muka hallara a wajen. muna kaiwa ga gaban ofishin, sai muka taras da an lalata kalandu da fostoci da ke a wurin gaba daya kuma shigar mu a ofishin sai muka taras da an daure maigadin kuma an kwace masa wayoyin sa biyu”.

“Wannan halin banza ce kuma muna kira da shugabanci su dauki babban mataki don dakatar da irin wannan halin ta’addacin” in ji Ogunkua.

Karanta kuma: Rundunar sojojin Najeriya sun ci nasarar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke yankin Baga a Jihar Borno