Uncategorized
Zamu yi iya kokarin mu wajen bayar da kai ga komai don kungiyar Biafra – Nnamdi Kanu

Babban Shugaban kungiyar ‘yan Iyamirai da aka fi sani da ‘Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya gabatar da cewa kungiyar zata yi iya kokarin ta da bayar wa na kowace iri domin ganin cewa kungiyar Biafra ta tabbata.
Naija News ta sami tabbacin wannnan furci na Kanu ne a yayin da yake jawabi a gidan rediyon Biafra a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban IPOB ya ce, bayyanuwar Jamhuriyar Biafra ta zama dole ne saboda ‘yan jama’ar su ta sha wahala sosai har ma da kunyatawa ta karshe.
Fadin sa a gidan radiyo na kamar haka:
“Sunana Nnamdi Kanu, Nine shugaban Kungiyar ‘Yan Biafra, kuma da yaddar Ubangiji ba mutum ba, Biafara zata bayyana kuma zata kafu saboda mun sha wahala isasshe”.
“An nuna mana banbanci, an muzunta mu, a nuna mana kiyaya kuma har an sa mu jin kunya har ma bai mai bukatar taimaka mana, ba maza da suka isa magana aji su. Wannan ya isa, Kungiyar IPOB na ashirye don hakan, kuma tabbas zamu ci gaba da yadda wannan kafuwan mu.
“Za mu ci gaba da yada wannan bisharar saboda Ubangiji ya aiko mu ne don hakan kuma dole ne mu aikata ayukan da aka aike mu da shi, ko da yaya kuwa.
Kamfanin Naija News ta gane da cewa Nnamdi Kanu da dadewa ke jagoran wannan kungiyar don ganin sun nasara da kasar Najeriya wajen wannan gwagwarmaya.
Naija News ta ruwaito a baya da cewa Shugaban Kungiyar ‘Yan Biafra, Nnamdi Kanu ya ce zai yi gabatarwa daga kasan Israila ga duniya duka game da Shugaba Muhammadu Buhari.
Karanta Kuma: Hukumar INEC ta gabatar da Sharidu da Matakai bakwai 7 ga zaben 2019 da ke gaba.