Labaran Nishadi
An yi wa Shahararen Dan Wasan Kwallon Najeriya, Kanu sata da barna
Sananan tsohon dan wasan kwallon kafan Najeriya, Kano Nwankwo ya bayana bacin ran shi game da irin barna da sace kayakin sa da wasu ‘yan fashi suka yi.
Rahoto ta bayar da cewa ‘yan fashi da babu wanda ya san su sun fada wa gidan tsohon dan wasan kwallon kafa, Kanu Nwankwo, inda suka kwashe kayakin adon gidan, harma da kyautannai masu tsadar gaske da ya samu a lokacin da ya saura da wasan kwallon kafa.
Gidan dan kwallon da ke a hanyar Waziri, a nan Victoria Island ta birnin Legas, inda ya ajiye wadannan kayakin, da kyautuna da ya samu sakamakon kwarewansa a fagen wasan kwallon kafa.
“A gaskiya ina da bacin rai sosai game da wannan irin mumunar abin, lokacin da na ke wasan kwallon kafa na bawa al’uman Najeriya farin ciki kuma sun yi fahariyya da yanayin wasa na. Abin mamaki ne gareni da ganin cewar akwai ‘yan kasar nan da har zasu iya aiwatar da irin wannan halin a gareni” in ji Kanu.
Gidan Nishadin nawa an kulle shi ne tun shekara ta 2015 don wata matsala da ke tsakanin Gidan nishadin da wata banki da aka fi sani da ‘Sky Bank’ akan wasu zargi da aka yi karar a Kotun koli da ke a Ikoyi, Jihar Legas.
Mun samu tabbaci da cewar Kanu na kasar Landan ne tun zuwan sa don bikin Krisimati, daga can ya samu kira daga nan Najeriya akan abin da ya auku da gidan nishadi, da cewa wasu sun fada wa ginin da kafa mata sabon tsari. Daga nan sai Kanu ya kamo hanyan sa zuwa Najeriya don tabbatar da wannan mugun aikin.
“Gaskiya, abin ya zo mani kamar mafarki saboda ban yi zaton haka ba” ruwa sun fado daga idannun sa a yayin da yake bayyana abin da ya faru ga manema labaru.
“Ba zata za a yi mani irin wannan cin mutunci ba” ko da shike ana kara bata kare ba akan gidan nishadin, kuma har yanzu ban karbi bayani ba daga kotu na tabbatar da cewa an karbi wajen daga hannnu na, amma ganin irin wannan mumunar abin, gaskiya ban ji dadi ba kuma hakan bai dace da ni ba” in ji Kanu.
“Har ma da Motoci da ke kewayen gidan nishadin duk a tafi da su, bamu san ma ko ta ina ne zamu fara neman wadannan kayan da dukiyar ba” in ji Shi.
Karanta Kuma: