Connect with us

Labaran Najeriya

Babban shugaban Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Idris ya yi ritaya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Baban gwagwarmaya da jaye-jaye, da rashin amincewar ‘yan adawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da IGP Ibrahim Idris don ya huta daga aikin tsaron kasar. Kamar yadda doka ta bayar, shekaru 35 ne kawai ma’aikaci zai yi a aikin sa a kasar Najeriya, bayan shekarun na sun cika sai mutumin ya yi ritaya.

Mun na da tabbacin wannan ci gaban ne a Naija News kamar yadda aka sanar a yau da cewa an sanya AIG Adamu Mohammed a matsayin sabon Mai rikon kwaryan babban shugaban jami’an tsaron ‘yan sanda.

Tsohon shugaban jami’an, IGP Idris zai cika shekaru 60 da haifuwa a ranar 15 ga watan Janairu. ya kamata ne shugaban ya yi ritaya tun ranar 3 ga watan Janairu, 2019 bayan ya cika shekaru 35 wajen aikin tsaron kasar. IGP ya shiga Hukumar Jami’an tsaron kasar ne a shekara ta 1984 da ta gabata.

Rahoto ta bayar da cewa kamin IGP Idris ya yi ritaya, ya sami ganawa da shugaba Muhammadu Buhari na tsawon awowi 2 a anan cikin fadar shugaban kasa a babban birnin tarayyar kasar, Abuja.

An sami sani da cewa kuma shugaba Buhari ya yi wata ganawa na neman shawara daga babban alkalin shari’ar kasar akan ko kila ya daga lokacin ritayar tsohon shugaban jami’an ‘yan sandan.

Adamu Mohammed, sabon shugaban Jami’an tsaron ya kasance Kwamishanan jami’an ne na Jihar Ekiti a inda aka daga shi da kara masa matsayi na zaman mataimakin shugaban jami’an tsaron kasar gaba daya.

Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya nada tsohon shugaban tsaron, IGP Idris ne a ranar 21 ga Watan Maris, shekara ta 2016 da ta wuce, bayan dakatar ta tsohon shugaban tsaron, Solomon Arasa daga matsayin.

Wannan nadin ya biyo baya ne ganin irin rashin amincewa da hukumomi da jam’iyyar PDP ta nuna akan barin shugaban ya cigaba da matsayin sa bancin lokaci ya kai da yakamata ya sauka.

Karanta kuma: Mahara sun kai farmaki a yankin Jema, Jihar Kaduna har sun kashe mutane Uku, kuma sun yi wa mutane kadan raunuka.