Connect with us

Labaran Najeriya

Duk masu kokarin kafa kiyayya tsakani na da Buhari za su sha kunya – inji Amosun

Published

on

at

advertisement

Gwamna Ibikunle Amosun, Gwamnan Jihar Ogun ya ce wasu mutane na shirin kafa kiyayya tsakanin shi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Amosun ya fadi wannan kalaman ne a yayin da yake gabatarwa a shiyar Kajola a Yankin Obafemi Owode a inda yake gudanar da yakin neman zaben sa ga zaben takarar dan Majalisar Tarayya a zaben 2019 da ke a gaba. ya ce” Duk masu kulle-kulle don jawo kiyayya tsakani na da shugaba Muhammadu Buhari za su sha kunya” in ji Amosun.

A yayin da yake gudanar da gabatarwan sa wajen yakin neman zaben, Amosun ya umurci magoya bayansa da cewa su yi kokarin jefa wa shugaba Buhari kuri’ar su, ya kara da cewa shugaban ya yi kokari da gaske wajen kawo cigaba ga kasar musanman ma ga Jihar Ogun.

Naija News ta ruwaito da cewa Manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar sunyi wata Ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja inda suka gabatar da goyon bayan su ga shugaban, sun ce “muna bada gaskiyar cewa Allah zai taimake ka da gwamnatin ka kuma” inji shugabanan Jihar Borno”.

“Duk shirin da suke yi, suna yin shi ne don kawo jayayya da kiyayya tsakani na da shugaba Buhari, babu kuwa wanda zai iya juwa bayan mu ko kawo wata kiyaya” in ji Gwamnan.

“Ina ne suke duka lokacin da tattalin arzikin Jihar ta lallace, ina ne su ke lokacin da hanyar jirgin kasan jihar ta lake, amma yanzu suna kokarin nuna kiyaya ga shugaban, bayan irin kokari da gwagwarmaya da yayi wa Jihar, ku zabi shugaba Buhari kuma ku goya masa baya” in ji Shi.

 

Karanta kuma: Matar Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta bukaci Mata da Matasa su sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a zabe na gaba.