Connect with us

Labaran Najeriya

Ga sabuwa: Shugaba Buhari ya gabatar da sabuwar takardan tafiya kasan waje

Published

on

at

advertisement

A ranar Talata 15 ga Watan Janairu 2019, A Gidan Majalisar Dokoki da ke Aso Rock, a birnin Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon takardan tafiya zuwa kasar waje da aka tsarafta.

Muna ta tabbacin hakan a Naija News da cewa an mika wa shugaba Muhammadu Buhari takardan ne daga hannun Babban Comptroller Janar na Hukumar kadamar da Tafiye-tafiyen kasa (NIS), Mohammed Babandede.

Taron da aka yi a birnin Abuja ta halarci Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo da kuma Ministan Harkokin Gida, Abdulrahman Dambazzau, Ministan ya bayyana da cewa sabuwar salon zai magance matsalolin sace-sace takardan tafiya da kuma wasu matsaloli da ake samu wajen samun takardan tafiya zuwa kasan waje.

Ya kara da cewa “Mun yi nisa da shiri don shirin wannan takardan ga kasa hade da taimakon Hukumar Tsaron Kasa ta wajen tsarrafa wannan takardan, da kuma ta wajen karuwa da aiki a kasar, da kuma samar da fasaha wajen aikar da tattalin airziki da dai sauransu” in ji Dambazzau.

Babandede, shugaban Hukumar NIS ya kara da cewa akwai banbanci kusan Ashirin da biyar 25 tsakanin takardan da ake amfani da shi a da, da kuma wannan sabon takardan.

A bayanin sa ya ce, Takardan ya kasu kala ukku ne:

  • Na farko na da shafi 32, kuma za ka iya amfani da shi ne tsawon shekaru biyar (5yrs, kudin samun takardan kuwa shine Naira dubu N25,000 a kasar Najeriya, A kasar wajen kuma zaka iya samun shi Dala $130
  • Na biyu kuma na da shafi 64, kuma za ka iya amfani da shi ne tsawon shekaru biyar (5yrs), kudin samun wannan kuma itace Naira dubu N30,000 a kasar Najeriya, A kasar waje kuma zaka same shi ne Dala $150
  • Na Ukku kuma shi ma na da shafi 64, kuma za ka iya amfani da shi ne tsawon shekaru goma ne (10yrs), kudin samun wannan kuwa shi ne naira dubu N70,000 a kasar Najeriya, A kasar waje kuwa zaka sameshi a dala $230.

Shugaban ya bayana cewa Hukumar za ta fara sayar da takardan ne watan Fabairu da ke gaba, kuma wadanda ke da tsohuwar zasu ci gaba da amfani da shi har lokacin da za a dakatar da ita kowa ya koma wa sabuwar takardan.

Akwai wasu manyan shugabannai kuma da suka halarci wannan hidimar.

 

Karanta kuma: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a gidan gadon babban shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki a makon da ta gabata a garin Ilorin, Jihar Kwara.