Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba 16, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 16 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Buhari da Osinbajo zasu halarci wata zama a gidan Telebijin a yau

Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo (SAN) za su kasance wajen wata zama na tsawon awowi biyu (2hrs) da za a gudanar a wata gidan telebijin a yau Laraba 16 ga watan Janairu.  An sami sanarwan ne daga bakin shugaban sadarwa ga Jam’iyyar APC, Festus Keyamo (SAN) wanda ya bayar a ranar Talatar da ta gabata ga manema labaran Naija News, ya ce, taron zai kasance ne a Gidan tattaunawa na Ladi Kwali, da ke a Sheraton Hotel a birnin Abuja.

2. Ana bikin yabawa da girmama wa ga Jaruman Najeriya da suka tafi

Shugabannin Najeriya da shugabannin ma’aikata na a birnin Abuja don bikin tunawa da rundunar sojoji ta shekarar 2019. An bukaci Shugaba Muhammadu Buhari don nazari akan farati da kuma halartar gudanarwan taron da ake yi.

3. An ci gaba da yajin Aiki a yayin  da kungiyar ASUU bata kai ga yarjejeniya ba da Gwamnatin Tarayya

Yan kungiyar Mallaman Jami’ar kasar Najeriya (ASUU) sun ki amincewa da shiri da kuma matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka don kawo karshen yajin aikin da suka fara tun watannai da suka wuce. An bukaci shugabannan kungiyar don bayyana matsayinsu a fili a yau ta hanyar mika rahoto game da tattaunawar su da membobin tarayya ga gwamnatin tarayya.

4. An bada tabbacin Mohammed Abubakar Adamu a matsayin mai rikon kujerar IGP

Babban Insfektan Jami’an ‘Yan Sanada, IGP Ibrahim Kpotun Idris, NPM, mni ya yi ritaya a ranar jiya 16 ga watan Janairu 2019 daga aikin’ hukumar tsaron Yan sandan Nijeriya da shekaru 60. Baban kwamanda da hukumomi da Jami’un kasar Najeriya, watau Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurni ga tsahon shugaban IGP Ibrahim Kpotun Idris, NPM, mni da cewa ya mika kujerar ga Mataimakin Insfekta Janar na’ yan sanda, AIG Mohammed Abubakar Adamu, Mni a matsayin tsabon shugaban Jami’an tsaron ‘yan sanda.

5. Hukumar EFCC ta bayyana batun fada wa gidan babban Alkali CJN Onnoghen

Hukumar ta EFCC ta yi watsi da kuma rashin amincewa da fade-faden da yankunan ke kai da kawo wa da cewa sun hukumar ta mamaye gidan babban alkalin Najeriya, Walter Onnoghen. Naija News ta bayar a baya da cewa yanar gizon nishadi ta watsa ko ta ina a ranar Talata da ta gabata da cewa hukumar EFCC sun mamaye gidan babban Alkalin.

6. Tsohon Mataimakin mai Yada yawun gidan Majalisar Jihar Kwara yayi janye daga Jam’iyyar PDP

‘Yan kwanki kadan da zaben shekarar 2019, tsohon Mai yada yawu na gidan majalisar dokokin Jihar Kwara, Hon Mohammed Suka-Baba ya yi murabus da Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar APC. Tsohon kakakin yada yawun ya bar Jam’iyyar ne tare da wasu mambobin Jam’iyyar PDP da ke yankin Kaiama ne anan Jihar Kwara.

7. Zaben shugaban kasa na 2019 zai kasance da ruduwa – inji Annabcin Nwazuo

Zaben shugaban kasa da za a gudanar wata na gaba zai kasance da ruduwa, in ji fadin Annabcin Emmanuel Ezenwa Nwazuo, shugaban wata Ikklisiya da ake kira da (Revolution Fire Christian Ministry – RFCM). Naija News ta ruwaito da cewa Annabi Nwazuo ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da Annabin sa na shekarar 2019, inda ya bayana da cewa ya gan cewar an gabatar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben sa’anan kuma zai ga shi an mika hannun Atiku Abubakar sama da cewar shi ne ya ci zaben.

8. Kungiyar CUPP sun bayanan muhinman matsaloli da ya kamata sabon IG na ‘yan sanda ya bawa kulawa

Kungiyar tarayyar ta Jam’iyoyin Siyasa sun bayyana matsaloli da ya kamata sabon shugaban ‘yan sanda IGP Mohammed Adamu ya fara nuna wa kulawa ta gaggawa. Kungiyar, wadda ta ƙunshi jam’iyyun adawa ta bukaci kulawa ta gaggawa, musanman ga dan siyasa kamar Senator Dino Melaye da mai yaki da kare hakkin al’umma, Deji Adeyanju.

9. Ana barazanar tsige Theresa May a yayin da MPs ta nuna rashin amincewa da shirin ta

Firayim Ministan kasar Birtaniya, Theresa May ta fuskanci baban mumunar rashi a kasar wanda bai taba faruwa ba a tarihin kasar. Majalissar sun bayyana a fili da rashin amincewar su da shirin ta na Brexit ta wajen fiye ta da kuri’u 230. ‘Yan majalisar sun bayyana da sauri don tabbatar da cewa basu bada goyon baya ba da yarjejeniyar ga shirin May, duk da cewa akwai kwanaki 72 da ta saura kamin tsige Birtaniya daga takar EU.

10. Ana shirin fara wasar nishadi ta shafi na BBNaija na 4 a Najeriya

Mai shiryawa na shafin nishadin (BBNaija) ya bayyana da cewa za a fara shafi na hudu na wasar BBNaija da aka saba nunawa a talabijin a kasar Najeriya. Wannan bayanin ya nuna da cewa ba za a yi shirin ba a kasar South Afirka kamar yadda a ka saba yi, za a yi shi ne a Najeriya wannan karon.

 

Samu cikaken labarai a NaijaNews Hausa

Advertisement
close button