Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: An sace Kwararren Kocin kwallon kafa, Abdullahi Biffo a Jihar Katsina

Published

on

at

advertisement

Abin kaito, duk da irin kokari da jami’an tsaron kasar ke yi don magance ta’addanci, sace-sace da kashe-kashe a kasan nan, masu aikata wadannan mugun halin basu daina ba, kullum sai karuwa suke.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Katsina, Gwamna Masari ya yi kira da cewa jihar na cikin kangin ‘yan ta’adda, kuma ya bukaci taimako ta musanman daga gwamnatin tarayya da jami’an tsaron kasar

Naija News ta samu rahoto da cewa an aikata wani mumunar hali kuma a Jihar, an sace wani babban koci na wasan kwallon kafa, Abdullahi Biffo wanda ke jagoran wata babban kungiyar ‘yan wasan kwallon kafar Jihar ‘Katsina United’. 

Akwai sani da cewa kocin shi ne ke jagoran ‘Babban Taken Wasan Kwallo ta Najeriya’ (NPFL) na ‘yan wasan kwallon ‘Katsina United’. An kuma bayar da cewa wadanda suka sace shi na bukat Naira Miliyan goma sha biyar (N15m) kamin su sake shi.

Naija News Hausa  ta ruwaito a ranar jiya kamar yadda muka samu labari da cewar wasu sun yi wa Shaharraren tsohon dan kwallon kafar Najeriya, Kanu Nwankwo barna a wata gidan karban bakin sa da ke birnin Legas, inda suka kuma kwashe masa kyautannai da ya samu duka a fagen wasan kwallon kafa lokacin da ya saura da buga kwallo.

Yanar gizon twitter ta bayar da tabbacin hakan daga hannun wani mai suna Adepoju.

Takaitacen labarin na sa na kamar haka: A turance;

Ko da shike kungiyar ‘yan kwallon sun fada da cewa kocin ya tafi ne zuwa kasar Ingila don sana’a, amma wannan ba gaskiya ba ne kamar yadda suka fada.

Wanda ya bayyana wannan ya kara da cewa, wadanda suka sace Abdullahi Biffo sun bada umurni da cewa kada kungiyar kwallon su bayyana wannan ga manema labarai, sai har sun biya kudi an sake shi.

A halin yanzu, an ci gaba da bincike a kan wannan mumunar labarin.

 

Karanta kuma: Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana amincewa da fatan cewar Jihar Borno za ta komar da daukakar ta.