Connect with us

Uncategorized

Sojojin Najeriya sun ba wa mutanen Natsinta da ke Jihar Katsina Magunguna

 

Gwamnatin Najeriya daga jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa Jaruman tsaron Najeriya bikin girmamawa da kuma nuna kulawa ganin irin gwagwarmaya da kokarin da rundunar ta yi wajen yaki da ta’addanci a kasar.

Rahoto ta bayar da cewa rundunar sojojin Najeriya sun kira jama’ar yankin Natsinta da ke Jihar Katsina don basu magunguna da isasshen kulawa sakamakon wannan babban bikin girmamawa da tunawa da Rundunar Sojojin kasar a shekara ta 2019. Sojojin sun yi wannan kyakyawan shiri ne a ranar Talata da ta gabata a shiyar Natsinta, Katsina.

Babban shugaba na kulawa da samar da lafiyar jiki na rundunar sojojin, DHM Musa Muktar ya halarci wannan hidimar.

Mazaunin wannan wurin sun samu kulawa ta gaske da kuma magunguna na kwarai dabam dabam, kamar gidan sauro, maganin zazzabi, maganin ciwon sauro, maganin hawan jini, maganin ciwon siga da de sauransu.

Shugaba DHM Musa Muktar ya ce, Wannan shirin da an yi shi ne don tsohin ma’aikata da suka yi wa kasar bauta, amma daga baya muka bude dama ga duk wanda ke murna da bukatar wannan kulawar don cika daya daga cikin gurbin hukumar.

Jama’ar sun ji dadin wannan shirin, harma a cikin su an sami wata da ta tabbatar da wannan, mai suna Mary Ibe.

“Ba a karbi ko taro daga hannun na ba ga magungunan da aka bani harma da gidan sauro” in ji ta.

 

Karanta kuma: Hukumar INEC ta fito da Fom na daukar Mallaman gudanar da aikin zaben 2019 da ke gaba.

 

Advertisement
close button