Labaran Najeriya
2019: Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya don su zabe shi ga zabe na gaba
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar Najeriya da cewa kada su zabi dan adawan sa Atiku Abubakar dan takarar Jam’iyyar PDP, amma su zabe shi don ci gaba da nasarar da gwamnatin sa ta samar cikin shekaru da suka shiga mulki.
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 yace “Ba zan manta da yan Shirin Fim, Mawaka da Yan Nanaye ba” a Najeriya.
Ya kuma shawarci magoya bayan sa su don su jefa kuri’un su ga duk dan takara da ke karkashin Jam’iyyar APC.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wannan ne a ranar Laraba a birnin Lokoja, Jihar Kogi.
“Jam’iyyar PDP na son su koma mulki ne dan su ci gabaa aiwatar da cin hanci da rashawa a kasar, kamar yadda suka yi shekarun baya kamin muka shiga mulki a shekara ta 2015” in ji Buhari.
Naija News Hausa ta tuna da cewa Mataimakin Gwamnar Jihar Kaduna, Yusuf Bala ya ce yankin Kudun Jihar Kaduna za ta ba wa Muhammadu Buhari zabe kashi 90 cikin 100.
Shugaban ya bayana da cewa gwamnatin sa ta yi kokarin samar da hanyoyi, wutan lantarki, tattalin arziki da kuma wasu samfarorin dabam-dabam kuma na cikin kokarin yaki da ta’addanci, makirci da sace-sace, da kowace irin mumunar gudanarwa a kasar.
“Ina a shirye kuma don karasa da cin gaba a kasar, wajen samar da ayukan Fasaha, Tallafa wa gina makarantu, Jami’o’i da sauran su” in ji fadin shugaba Muhammadu Buhari.