Connect with us

Uncategorized

ASUU: Za a dakatar da yajin aiki lokaci kadan da nan – Minista Adamu

Published

on

at

Da tsawon watannai da dama da ta gabata, kungiyar Mallaman Makarantan Jami’a (ASUU) sun shiga yajin aiki da har ‘yan makaranta sun gaji da zaman gida.

Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ya yi kira ga mallaman makarantan jami’o’i duka da cewa su yi hakuri da gwamnatin tarayya akan wannan yajin aikin.

Mallam Adamu ya gabatar da wannan bayanin ne a bikin fitar jami’a ta 10 da aka yi a makarantar jami’ar Federal Polytechnic Offa, da ke nan Jihar Kwara a yau Alhamis 17, ga watan Janairu, 2019.

Ya ce “An kusa a kawo yajin aikin ga karshe”.

Adamu ya kara da cewa ana daukan matakai don magance wannan yajin aikin da ya dauki tsawon watannai da dama.

“Zaman lafiya abu ne mai muhimancin kwarai da gaske a jami’un mu, idan kuwa babu zaman lafiya ba yadda samar da ilimi zai ci gaba” inji shi.

Shugaban ya karshe da nuna godiyan sa ga ‘yan makarantan jami’a da mallamai duka da sauran ma’aikatan jami’a da irin hadin kai da samar da zaman lafiya a jami’u.

 

Karanta wannan: Dalilin da ya sa Mallaman Kwallejin Fasaha suka soma yajin aiki