Ban yi zaton zan fadi ga zaben 2019 ba – inji Shugaba Buhari

Ganin irin yabawa da goyon baya da kuma irin amincewa da jama’a suka nuna mana wajen yawon yakin neman zabe a yankunan kasar, “Zai zama da mamaki inji cewa na fadi zaben 2019” in ji Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari ya buga gaba da bada tabbacin cewar lallai bai da tunanin cewa zai fadi zaben shugaban kasa da ke gaba.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Atiku Abubakar ya kwanaki da suka wuce ya yaba wa Kungiyar Manyan shugabanan Jihar Borno (Elders Forum) don sakon da suka aika wa shugaba Buhari na cewar ya kamata shugaba Buhari ya dakatar da halin sakin ‘yan ta’adda da aka kama da laifi ko ta’addanci, “Wannan bai da ce ba” in ji Shugabanan Jihar.

A wata ganawa da aka halarci shugaba Muhammadu Buhari a jiya Laraba 16 ga watan Janairu, 2019 inda aka yi wa shugaban kasan tambaya da cewa, Shin yaya zaka ji idan an ce ka fadi zaben takarar shugabancin Najeriya da ke gaba?

“Na yi takara har sau ukku a kasar nan shekarun baya da suka wuce kuma ban ci zabe ba sai har karon da Hukumar gudanar da zabe INEC ta fito da sabon tsarin yin amfani da na’urar kadamar da zabuna, sai ga shi na ci zabee” in ji shi.

“Amma dai zai zama abin mamaki gareni har inji wai na fadi ga wannan zabe da ke a gaba” in ji Buhari, ganin irin goyon baya da yabawa da ake mani yankunan kasar nan.

Buhari ya fadi wannan ne a zaman da suka yi a wata gidan ganawa a birnin Abuja, inda aka gudanar da shirin nemar bayani daga ‘yan takara.

Karanta kuma: Shugaba Buhari ya gabatar da sabuwar takardan tafiya zuwa kasan waje

“Na fito takara shekarar 2003 ban ci ba, shekarar 2007 ma na fita kuma ban ci ba, harma shekarar 2011 duk na fito takara ban ci ga duk a lokacin ina kotu” na dauki hasara sai har shekarar 2015 Allah ya taimaka na ci kuma da taimakon Na’urar binciken katin zabe.

Gwamnatin mu na kokari da gwagwarmaya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma har da yaki da ta’addanci a kasar nan ba fasawa.

Samu cikakkun labaran Najeriya daga Naija News Hausa