Connect with us

Uncategorized

Cutar Lassa Fever: An samu rahoto da cewa wani Soja ya mutu a Jihar Jos

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta sami sabuwar labari yanzun nan da cewa wani Sojan Najeriya da ke a barikin Rukuba ta Jihar Jos ya mutu.

An sanar da cewa bayan ‘yan bincike da aka yi akan abin da ya kashe sojan, an iya gane wa da kuma tugumar cewa watakilan cutar ‘LASSA FEVER’ ne ya kashe shi a bisa alamun da aka samu.

Cutar LASSA FEVER wata mumunar cuta ne da ke a jikin bera, cutar ya kashe mutane da daman kwanakin baya a kasar harma a wasu kasashen waje.

Ko da shi ke ba a bayyana sunan sojan da ya mutu ba, amma mai yada yawun rundunar sojojin yankin, Mista Ikechukwu Stephen ya bada tabbacin wannan abin a yau Alhamis. Ya ce “Sojan ya mutu ne a asibitin Jami’ar Bingham da ke a nan Jankwano, a Jihar Jos” in ji shi a yadda aka ba wa manema labarai hirar abin da ya faru.

“Da farko dai an kai sojan ne a asibitin da ke yankin sojojin, daga baya aka kara gaba da shi zuwa babban asibitin Jami’ar Bingham a nan cikin Jos inda sojan ya dauke nunfashi” in ji Stephen.

“Mamaicin ya kamu ne da rashin lafiya bayan dawowar sa daga Jihar Kogi don jana’izan tsohon sa da ya mutu kwanakin baya”.

Sojan ya mutu ne a ranar 15 ga watan Janairu, 2019 bayan rashin lafiyar da ta rike shi da tsawon kwanaki hudu. Cikin binciken da aka yi, amma tugumar cewa sojan ya kamu ne da cutar LASSA FEVER, ganin irin alamun da ciwon ke dauke da shi.

“Babban Kwamandan rundunar da ke a yankin ya bada umurni da cewa a ci gaba da bincike da kulawa da mutane da ke yankin da kuma rundunar sojojin barikin don tabbatar da cewa babu wani kuma da ke kame da cutar” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa rundunar Sojojin Najeriya sun kira jama’ar yankin Natsinta da ke Jihar Katsina don basu magunguna da isasshen kulawa sakamakon babban bikin girmamawa da tunawa da Rundunar Sojojin kasar a shekara ta 2019 da Gwamnatin Najeriya ta gudanar.

Kalli wannan bidiyon: