Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 17, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 17 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni a saki babban Alkalin Najeriya CNJ Onnoghen

Gwamnatin tarayya ta bukaci Hukumar Bincike Asusun kudin Kasa (NFIU) da cewa su daskare asusun ajiyar kudi biyar da babban Alkalin, Walter Onnoghen ke da su.

Abubakar Malami, babban lauyan tarayya ya bayyana da cewa umurni ta zo ne daga shugabancin kasar na cewar a daskare asusuwan har lokacin da za a kare bincike akan babban alkalin, Walter Onnoghen.

2. IGP Adamu Mohammed ya nada Frank Mba a matsayin PRO na Hukumar

Sabon babban shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, Adamu Mohammed ya sanya Frank Mba a matsayin mai yada labarai ga jami’an ‘yan sandan kasar (PRO).

Wannan matakin ya bayyana da cewa Frank Mba zai dauki gurbin Jimoh Moshood wanda daman shi ne da wannan matsayin PRO na hukumar tsaron.

3. Zan sayar da kampanin NNPC koda hakan zai dauki raina ne – in ji Atiku

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana da cewa kamfanin NNPC na Najeriya an maida shi kamar ” kamfanin ‘yan Mafia”.

Dan takaran, Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar da wannan ne a yayin da ya ke jawabi a wata ganawa da kungiyar ‘yan kasuwancin Jihar Legas, in da yayi rantsuwa da cewa zai ba sayar da kampanin man fetur NNPC, ko da zata dauki ran sa ne idan har ya hau mulki shekara ta 2019

4. A ƙarshe, CCB ta yi wa CJN Walter Onnoghen hidima

Hukumar (CCB) ta ci nasara a karshe ga zargin aikata laifuffuka da aka yi wa babban alkalin kasar, Walter Onnoghen.

Ganin wannan ci gaban, an bukaci alkalin ya halarci zaman kotun (CCT) wadda aka dakatar har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2019.

5. Kotun ta yanke hukuncin bayar da kudi N2.2b da aka ribato daga tsohon shugaban Sojojin Sama, Adesola Amosu ga Gwamnatin tarayya

Alkalin shari’a, Mojisola Olatoregun na Kotun Tarayyar Tarayya da ke a birnin Legas ta umarci kaddamar da kudi Biliyan (N2.2b) da aka ribato daga tsohon Shugaban Sojojin Sama, Air Marshal Adesola Amosu zuwa ga aljihun Gwamnatin Tarayya.

6. Za a gabatar da tsarin sabon albashin ma’aikata kasa ga Hukumar NEC a yau

Gwamnatin tarayya zata gabatar da sabon tsarin albashin ma’aikata N30,000 ga Majalisar Tattalin Arzikin kasa a yau Alhamis don ƙarin tattaunawa.

Wannan shi ne sakamakon ganawar da majalisar zartarwar tarayya tayi a daren ranar Talata a birnin Abuja.

7. Gwamnatin Tarayya ta ci bashin kudi N6tr daga asusun ‘yan fensho

Gwamnatin Tarayya ta ari kudi kimanin Naira Tiriliyan (N6.16tr) daga cikin naira tiriliyan N8.49tr na aljihun kungiyar Fensho.

Shugaban Kungiyar ‘yan Fensho ne ya bada wannan kasafin a ranar Talatar da ta gabata a birnin Abuja inda aka bayyana da cewa Gwamnatin tarayya ta ari kashi 73.5% cikin dari 100% na asusun fensho.

8. Hukumar EFCC ta gayyaci Fani-Kayode da Odumakin akan yada labarun karya

Hukumar EFCC ta yi kirar gayyatan tsohon ministan harkokin kasa, Femi Fona Kayode da Yinka Odumakin, babban hafsan kungiyar Afenifere don zu so su bayyana zargin da suka yi wa hukumar na cewar hukumar na ƙoƙarin kame babban alkalin kotun Najeriya, Walter Onnoghen.

Tony Orilade, mai magana da yawun hukumar ya sanar da wannan ne a taron manema labaru na Najeriya (OPAN) a birnin Abuja.

9. Yemi Osinbajo ya bayyana bakin cikin sa game da gwajin da aka yi wa Alkali Walter Onnoghen

Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayyana bakin ciki shi da gwajin shari’ar babban alkalin shari’ar Najeriya (CJN), Walter Onnoghen game da zarge-zargen da aka yi wa alkalin na rashin gabatarwa da cikaken kasafin asusun kudin sa.

Osinbajo ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari bai san da wannan shirin gwajin ga alkalin ba sai har da maraicen asabar da ta gabata.

10. An gabatar da sakin Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo daga karar laifin cin zarin bil’adama

An bada umurnin a saki tsohon shugaban, Laurent Gbagbo akan hukuncin kisa da aka yanka masa da wani mai suna Charles Ble Goude tsohon shugaban kungiyar matasa da aka bayyana a matsayin daya daga cikin ma’aikatan tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire.

 

Ku sami karin labarai a Naija News

 

Advertisement
close button