Connect with us

Uncategorized

Na rantse ko da za a kashe ni ne sai na sayar da NNPC – inji Atiku

 

Dan takaran shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku ya gabatar da shirin sa idan har ya ci zaben shugaban kasar Najeriya.

“Ina tabbatar maku da cewa zan sayar da samfarin NNPC” in ji shi

Atiku ya kara da cewa wani abin mahimi da zan yi kuma shine tabbatar da cewa na taimakawa abokai na da ganin cewa sun samu kudi isasshe.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya fada kamar haka a baya da cewa, “ba zani gudanar da shirin neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar kaman yadda gwamnatin da ta saba yi” da asusun kasar wajen gudanar da shirin yakin cin zaben su a shekarun baya.

Ya ce “Ba zan tara wa iyalai na arziki ba amma zan yi hakan ga abokai na”.

Dan takaran ya bayanna wannan shirin ne a ranar Laraba da ta gabata a lokacin da ya ke gabatarwa a Jihar Legas a wata zama da aka lika wa suna “Ribato da tattalin arzikin kasar Najeriya”.

A wannan zaman ne Atiku ya bayyana shirin sa na sayar da samfarin man fetur NNPC idan har ya hau mulki.

“Shin laifi ne abokai na su kasance da arziki? idan har ba cin hanci da rashawa ciki, wannan ba laifi bane” in ji Atiku.

Kalli bidiyon, inda Atiku ya gabatar da shirin sa ga kasar:

Karanta kuma: Wasu da ba a sansu ba sun sace Kwararren Kocin kwallon kafa, Abdullahi Biffo a Jihar Katsina

Advertisement
close button