Connect with us

Uncategorized

Na yi iya kokari na a mulki – in ji Tsohon IGP Ibrahim Idris

 

Babban shugaban Jami’an  tsaron ‘Yan Sandan Najeriya na da, IGP Ibrahim Idris (rtd) ya buga gaba da bayyana irin kokarin da ya yi a da da yake jagoran jami’an tsaron. IGP yace “Na yi iyakar kokari na lokacin da ni ke a kan kujerar shugabancin Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar nan”.

Naija News ta ruwaito da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da IGP Ibrahim Idris don ya huta daga aikin tsaron kasar, kamar yadda doka ta bayar, shekaru 35 ne kawai ma’aikaci zai yi a aikin sa a kasar Najeriya, bayan shekarun ta cika, sai mutumin ya yi ritaya.

Tsohon shugaban, IGP Ibrahim Idris (rtd), ya yi wannan bayanin ne a birnin Abuja a yayin da ya ke mika wa sabon shugaban Jami’an tsaron, IGP Adamu Mohammed matsayin sa kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurce shi da yi.

Ya ce “A lokaci na, na yi iya kokari na”.

Ibrahim ya kuma bayyana murnan sa da irin goyon baya da sauran shugabanan tsaron kamar su DIGs suka ba shi a lokacin da ya ke shugabancin hukumar. “Na gode wa irin sadaukarwa da goyon baya da kuka bani” na kuma godewa sauran darukan tsaron duka sosai, in ji Ibrahim Idris.

Ya kare maganan sa da cewa, “Ina maka fatan Alkhairi ga shugabancin hukumar”.

Ya fadi wannan ne a Edkwatan Jami’an da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

 

Karanta kuma: An sace Kwararren Kocin kwallon kafa, Abdullahi Biffo a Jihar Katsina

Advertisement
close button