Connect with us

Uncategorized

Ba tsaro kawai zamu samar da shi ba, harma kare damar al’umma – Ag. IGP Adamu

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Sabon shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, Ag. IGP Abubakar Mohammed Adamu ya bayyana gurin sa ga al’ummar kasar Najeriya gaba daya.

Mohammed da aka sanya matsayin babban shugaban ‘yan sanda bayan ritayar tsohon shugaban jami’un, Ibrahim Idris (rtd) ya aika fada da cewa mulkin sa zai kasance daban.

Naija News ta ruwaito da cewa tsohon shugaban Jami’an  tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris (rtd) ya buga gaba da cewa ya yi kokari da gaske a lokacin da yake jagoran jami’an tsaron. Ibrahim ya ce “Na yi iyakar kokari na lokacin da ni ke a kan kujerar shugabancin Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar nan”.

IGP Adamu ya ce;

“Ba tsaro kawai zamu samar da shi ba, harma da kare damar al’ummar Najeriya duka” in ji shi.

Ya gabatar da wannan ne a yanar gizon nishadanwa twitter da jami’un ke amfani da shi wajen samar da labaru.

labarin na kamar haka, a turance;

Ka tuna a baya, Kakakin Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, FPRO, Ag. DCP Jimoh MOSHOOD ya bada tabbacin cewa jami’an za su yi iya kokarin su wajen ganin cewa babu wata matsala ga Zaben 2019 da ke gaba.