Connect with us

Uncategorized

Barawo, a ko yaushe barawo ne – APC sun cewa Atiku

 

‘Yan Jam’iyyar APC da ke kasar Amurka sun yada yawu game da ziyarar da dan takaran shugaban kasan Najeriya ta Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi a ranar jiya.

“Barawo, a ko yaushe barawo ne” in ji APC Amurka.

Jam’iyyar sun ce, ziyarar Atiku ga Amurka bai can za matsayin sa na mara gaskiya ba. Atiku mai laifi ne kumar har gobe ba zai iya wanke kansa daga wannan ba.

Mun bayar a Naija News ‘yan lokatai da ta wuce da cewa dan takaran, Atiku Abubakar ya sami shiga kasar Amurka bayan ‘yan shekaru da dama da ta gabata. , yesterday arrived the US after 13 years, and for the first time since he left office as Nigeria’s vice-president.

“Barawo, barawo ne ko da ina ne ya shiga” in ji Mista Adeshegun Labinjo, ciyaman na ‘yan jam’iyyar APC da ke kasar Amurka.

Ya ce, ko da shike ba mu hana Atiku shiga kasar Amurka ba, “Matsayin shi da halin shi na mara gaskiya bai canza ba, ko da ina ne ya je kuwa” in ji Labinjo.

“Tarihi da bincike ya nuna cewa Atiku barawo ne, ya yi ta hada hannu da matarsa da ke zama a nan kasar Amurka shekarun baya da wajen cin zalunci da sace tattalin arzikin kasar Najeriya” Atiku dan son kai ne, kuma azalumi ne tun lokacin da ya ke matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya a lokacin da tsohon shugaba, Olusegun Obasanjo ke a mulki.

Duk da irin alkawalai da kokarin da dan takaran ya ke yi, ‘yan Najeriya da dama sun bayyana da cewa ba zasu jefa wa Atiku kuri’ar su ba, ko da shugaba Muhammadu Buhari na bakin mutuwa ne.

sakon na kamar haka, a yanar gizon nishadin twitter da wani ya aika wa Atiku.

 

Ku sami cikakkun labaran siyasa a Naija News Hausa

Advertisement
close button