Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari bai da karfi da kuma isashen lafiya da zai jagoranci Najeriya – ‘Yan Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tau ga wata sabuwa:

‘Yan Najeriya da dama sun nuna rashin amincewan su da shugaba Muhammadu Buhari akan cewa tsohon ya kai ga tsufa, kuma bai da cikaken lafiyar jiki da har zai kara shugabanci a kasar nan.

A ranar jiya, shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci yankin Warri, babban garin da ke a Jihar Delta don gabatarwa da yakin neman zabe a Jihar.

A nan ne shugaba Buhari yayi wata kuskuren kalamai a yayin da yake gabatarwansa a wajen taron, a inda ya gabatar da dan takarar Jihar da matsayin ‘shugaban kasa’.

Daga nan ne ‘yan Najeriya suka bi yanar gizon nishadin su da bayyana bacin ran su da kuma hangen su ga shugabancin kasar Najeriya.

Kadan daga cikin bayanan a yanar gizon twitter na kamar haka a;

https://twitter.com/dokitorsavage/status/1085645607031599105

Naija News ta ruwaito da baya da cewa tsohon Gwamnan Jihar Neja, Aliyu Babangida (Talba) ya ce “Ina tabbatas maku da cewa Atiku zai ci nasara kan Buhari a zaben 2019”  A wata jawabin sa da ‘yan jarida a Kaduna, tsohon gwamnan ya ce: “Ku yi imani da ni, ba kawai a jiha na ba, na yi imanin cewa idan zaben ba ayi juya-juya ko wata halin daru ba, tau na tabbata Atiku zai yi nasara da Buhari ga zabe na gaba.”

Haka kuma ‘yan Jam’iyyar PDP, a baya suka shawarci Buhari ya koma gidan sa a Daura yaje ya huta. sun fadi wannan ne wurin amsa wa rokon da Shugaba Muhammadu Buhari yayi na cewa ‘yan Najeriya su bashi lokaci kadan don ya kadamar da burin sa ga kasar. sun ce ba za a bada shugabancin kasa ba ga mutumin da kullum a na neman ya huta, bai da lafiya, ga kuma tsufa ya kawo.