Connect with us

Labaran siyasa

Ko da na sanya Paparoma abokin takara na, Kristocin Kaduna ba za su zabe ni ba – El-rufai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jama’ar Jihar Kaduna, musanman kristocin jihar sun nuna rashin amincewa da gwamnar Jihar, Nasir El-Rufai tun da dadewa.

Gwamnan ya bayyana a wata ganawa da yayi da manema labaran gidan telabijin ‘Channels Television’ a ranar Alhamis da ta gabata cewa ko da ya sanya Paparoma ne a matsayin abokin takaran shi kiristocin Jihar da wadansu da suka rigaya suka kudura a zuciyansu, ba za su zabe shi.

Muna da sani a Naija News da cewa El-Rufai ya zabi Hadiza Balarabe, ‘yar uwan sa Musulunma a matsayin abokiyan takaran shi ga zaben gwamnan Jihar Kaduna a zabe na gaba.

Ganin wannan, kiyaya ta tashi daga jama’ar jihar musanman kiristoci, da cewa wannan bai daidanta ba.

Rahoto ta bayar da cewa Kungiyar Addinin Krista ta Tarayya da wadansu sanannun mutane sun nuna rashin amincewa su da wannan matakin da El-Rufai ya dauka na sanya macce, musanman musulunma ‘yar uwansa a matsayin abokiyar takaran shi ga zaben gwamnan Jihar Kaduna.

Duk da kuwace-kuwace da bacin rai da jama’a suka nuna, gwamnan kuwa bai damu da wannan ba.

Ya ce “Wannan irin matakin da na dauka zai taimaka wa Jihar Kaduna wajen fahimtar manta da addini inda an zo ga maganan siyasa” in ji shi.

“Ko waye na zaba a matsayin abokin takarana, kai ko da Paparoma ne na zaba, Kristocin Jihar Kaduna ba za su zabe ni ba” in ji El-Rufai, saboda sun rigaya sun kudurta a zuciyarsu cewa ba za su so ni ba ko ta yaya.

Shekaru da daman da suka wuce, Kirista ne ke zaman mataimakin gwamnan Jihar Kaduna. Amma babu wata ci gaba da hakan ya kawo, kuma babu abin da wannan ya magance, kai harma Bala Bantex, tsohon mataimakin gwamnan jihar na da sun ki shi don ya fito takara daga Jam’iyyar APC.

Kai, harma mataimakina na yanzun da yake Kirista sun ki shi, kuma ni ban sanya shi ba dun ya na kirista. Na zabe shi ne don aboki na ne tun a makarantan jami’a babba, mai ilimi ne shi, kuma ya na da hangen nesa. Amma duk da haka, sun ki shi, sun raina shi kuma” in ji Gwamnan

Akwai matsaloli da daman da ba za a iya gane wa ba a Jihar a halin yanzun, bukata na ita ce “Jihar na cikin mawuyacin hali yanzun nan, mafita ne kawai muke nema don gyara jihar” in ji Nasir.

Naija News ta ruwaito da cewa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yi kira da cewa “Jihar Katsina cikin mawuyacin hali da irin hari da sace-sacen mutane da ake yi a Jihar” in ji Gwamnan.

Karanta kuma: Cutar Lassa Fever ta dauki ran wani Soja a Jihar Jos