Connect with us

Uncategorized

Mahara sun yi wa dan takarar Gwamnan Taraba na Jam’iyyar APC mumunar hari

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Taraba sun bada tabbacin mumunar hari da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa dan takarar Gwamnan Jihar daga Jam’iyyar APC, Sani Danladi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Sunday Onuoha, wani babban bishop ya bayyana a cikin gabatarwansa a wata zama da suka yi a birnin tarayya, Abuja da cewa “ba mamaki Boko Haram su fada wa Jihohin arewacin kasar, kamar Bauchi, Taraba, Gombe da kuma Adamawa” in ji shi.

Mun sami rahoto da cewar Gwamnan ya kama hanyar Wukari ne zai je yankin Ibi don gudunar da yakin neman zabe. Suna aka tafiyar ne da darukansa sai ga ‘yan ta’adda kwaram da hari.

A fadin wani da yake shiyar a lokacin da mumunar abin ya faru, ya ce “Motoci shidda ne aka kone kurmus da wuta, abin ya dauki tsawon awowi biyu.

An bayyana da cewa Wukari na da kilomita 270km ne kawai da babban birnin Jihar, watau Jalingo.

A halin yanzu mun sami sani da cewa Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ya kafa kulle na tsawon awowi goma sha biyu (12hrs) a Wukari har sai an kai ga gane abin da ya faru, kuma an karshe bincike.

Kwamishanan Jami’an ‘yan sandan Jihar, David Akinremi ya bayyana ga maneman labarai da cewa “Gwamnar na kan hanyar zuwa yankin Ibi ne a lokacin da mahara suka fada masu da wannan mumunar harin”.

“An kafa kullen shiga da fitan awowi goma sha biyu ne don tabbatar da cewa an dakile duk wata shiri na irin wannan mugun hari a Jihar”.

Mun kuma samu labari da cewa wani Anbasadar kasar nan, Hassan Ardo Jika ya tsira ne da mumunar harin da kyar.

Jami’an tsaro na kan bincike don kare gane sanadiyar wannan harin da kuma tabbatar da cewa an dakile duk wata shiri na gaba.

 

Karanta kuma: Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya dakatar da yawon yakin neman zabe a Jihar