Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Buhari zai ziyarci Jihar Borno a yau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Jihar Borno ta gabatar da yau litini 21 ga watan Janairu a matsayin ranar hutu daga aiki don girmama wa ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Jihar.
Mun sami rahoto da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Borno a yau litini, ganin wannan an dakatar da ma’aikata duka yau daga zuwa ofishoshin su ga aiwatar da ayukan su kamar yadda suka saba.

Naija News Hausa ta samu sani a bayar da cewa wasu ‘yan Najeriya sun ce Buhari bai da karfi da kuma isashen lafiya da zai jagoranci Najeriya

“Ina sanar maku da cewa an sanya da kuma dakatar da ma’aikata duka da ga aikin su a ranar Litini 21 ga watan Janairu, 2019 don fitowa da marabtan ziyarar da shugaban kasar Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari zai kawo wa Jihar don kadamar da shirin yakin neman zabe a Jihar” in ji Kwamishanan Labarai, Dokta Mohammed Bulama a wata gabatarwa da yayi jiya Lahadi, ga watan Janairu, 2019.

“An bada wannan hutun ne ga ma’aikatan gwamnati da na aikin dayantaka, ‘yan makaranta da ‘yan kasuwa don samun marabtan shugaba Muhammadu Buhari a yayin da yake shigowa” in ji shi.
Ya kara da cewa, kowa za ya koma wa aikin sa ranar Talata 22 ga watan Janairu, 2019 bayan wucewar shugaban kasar, Muhammadu Buhari.

Karanta wannan: ‘Yan ta’adda sun yi wa dan takarar Gwamnan Jihar Taraba daga Jam’iyyar APC, Sani Danladi wata mumunar hari.