Connect with us

Labaran Nishadi

Atiku na iya jagorancin Najeriya, amma ba tare da Peter Obi ba – in ji Omatsola

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani babban fasto na wata Ikklisiya da ke yankin Lekki a Jihar Legas, Manzo Chris Omatsola wanda aka zarga da wata laifin fyade shekarar da ta wuce ya ce “Ba wata alamar nasara ga Atiku Abubakar, idan har Peter Obi ne abokin takaran shi ga wannan zaben tarayya da ke gaba.

Omatsola ya bayyana wannan ne a lokacin da yake anabcin sabuwar shekara ta 2019.

Mun sami sani a Naija News da cewa manzon ya fada da cewa Nasara ba zai tabbata ga Atiku ba mudin Peter Obi ne ya sanya a matsayin abokin takaransa ga wannan zaben, ya ce “Hakan ba da ga Allah ba ne” in ji shi.

“Atiku Abubakar na iya jagorancin kasar Najeriya amma ba tare da Peter Obi ba” in ji Manzo Omatsola. Ya kara da cewa duk da cewa hadin su biyun ya bayyana ga jama’a kamar hakan ya dace, amman wannan ba shirin Allha ba ne.

“Atiku aboki na ne amma gaskiya dangantakar shi da Peter Obi bai da ce da shi ba kuma ba zai taimaka wa takarar sa ba” in ji Manzo Chris Omatsola.

Ko da shike ‘yan Najeriya sun nuna bacin ran su game da matakin da Atiku ya dauka na rashin halarta zaman muhawarar takaran shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Atiku ya bayyana dalilin da ya sa bai iya tsayawa ga muhawarar ba, kuma da baya ya aika da hankuri ga masoyansa da ‘yan Najeriya gaba daya da cewar shi ma bai so hakan ba amma yin hakan na da dalili.

Sakon a yanar gizon nishadin twitter ya bayyana wannan.