Connect with us

Labaran Nishadi

Dr. Amina Abubakar Bello Sani Bello ta ba wa Mata 150 tallafin kudi na 10,000 ga kowanansu a Mariga, Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Matan Gwamnan Jihar Neja, Dokta Amina Abubakar Sani Bello ta bawa mata 150 tallafin kudi na dubu goma N10,000 ga kowanen su.

Naija News Hausa ta samu sani daga yanar gizon nishadi ta Facebook wanda babban sakataren yada labarai ga ciyaman na yankin Mariga a Jihar Neja, Dauda Alhaji Shehu ya watsar da cewa matan gwamnan Jihar Neja ta bada tallafin kudi N10,000 ga mata kimanin dari da hamsin a yankin.

An gudanar da wannan hidimar ne a ranar Lahadi 20 ga watan Janairu da ta gabata a yankin Mariga, daya daga cikin hukumomin Jihar Neja.

“Wannan hidimar, hanya ce na nuna godiya da kuma murna ga Allah don rai da lafiya da ya bayar, da kuma godiya da yabawa ga gwamnatin Jihar Neja ga irin goyon baya da kulawa da ta yi wa mutanen yankin mu cikin shugabancin su na tsawon shekaru Ukku da ta gabata harma ta wurin matar Gwamnan Jihar, Dokta Amina Abubakar Sani Bello da irin kulawa da ta nuna musanman ga matan yankin mu” in ji fadin Matan Ciyaman din yankin Mariga, Hajiya Hassana Abdulmalik Sarkin Daji a yayin da take gabatarwa da mika wa matan wannan tallafin kudi da aka bayar garesu don taimakawa ga tattalin arzikin su da kuma karfafa kasuwancin matan.

“Daya daga cikin manufan Gwamnatin Jihar itace ganin cewa an samar da kulawa mai dacewa ga Mata da kuma tallafa masu don karfafa gwuiwarsu da cinma gurin su” in ji babban mai bada shawara fasaha ga gwamna, Alhaji Aminu Bobi.

Naija News ta ruwaito da cewa Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello ya sanya hannu ga dokar kasafin kudi ta shekarar 2019 kwanakin baya da ta wuce a fadar Gwamnatin da ke a Minna, babban birnin jihar.

Jibrin Baba Ndace, Babban Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, ya shaida wa manema labaran Naija News cewa Gwamna Sani-Bello ya yaba wa goyon bayan da majalisar dokokin jihar Neja ta bayar ta amince da wannan kasafin, ya ce “wannan shi ne kari na farko da muke sanya hannu ga kasafin kuɗi a watan Disamba”.

A cewar shi, “Wannan ya nuna irin amincewa da babban buri da mambobin Majalisar ke da ita kan Jihar. Har ila yau, wannan na nuna dangantakar da take tsakanin Babban Jami’in Dokoki Jihar ke da ita da Mambobin Jihar. ”

“Matar yankin Mariga sun bayyana murnan su da wannan ci gaba da kuma irin kulawa da tallafi ta musanman da gwamnatin Jihar ke bayar wa ga matan yankin Mariga”.

Hajiya Hassana ta umurci matan da aka bawa tallafin da cewa su yi amfani da kudin a hanya da ta dace don taimaka wa zaman rayuwar su.

“Ina godewa duk wandanda suka nuna mana goyon baya, idan ba da goyon bayan ku ba, da ba zamu kasance a nan ba” in ji Hajiya Hassana.

 

Ka sami cikakkun labarai a shafin Naija News Hausa

Karanta kuma: Barawo, a ko yaushe barawo ne , Jam’iyyar APC sun gayawa Alhaji Atiku Abubakar dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP.