Labaran Najeriya
Hidimar Shugaba Muhammadu Buhari a Maiduguri, Jihar Borno
Mun sami hirar shigar shugaba Muhammadu Buhari a birnin Maiduguri kamar yadda muka bayar da safen nan cewa Gwamnar Jihar Borno ya bada hutu ga ma’aikata da ‘yan makaranta a ranar yau, Litini 21 ga watan Janairu don karban shugaban Muhammadu Buhari zuwa Jihar.
Shugaban ya samu hallara daga jirgin sama a Jihar dadai karfe goma 10:30 da rabi na safe.
Turkin mutanen Jihar sun fito, Yaro da babba, mata da maza, shugabannai da almajirai duka don karban shugaba Muhammadu Buhari.
A saukar sa, Adams Oshiomole shugaban Jam’iyyar APC na tarayya ne ya fara karban shugaban tare da wasu kuma da suka halarci wannan ganuwar, kamar; Maj. -Gen. (rtd) Babagana Monguno, Ministan Harkar Jiha Alhaji Baba Shehuri da wadansu manyan shugabanan Jihar da wadanda suka biyo shugaba Buhari a baya.
Gwamnar Jihar, Kashim Shettima ya halarci karban shugaban, ‘Yan Gidan Majalisar Tarayya da Majalisar dokokin Jihar duk sun halarci wanan hidimar.
Mun kuma samu labari da cewa shugaban ya ziyarci darukan sojojin Najeriya da ke yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar don nuna kulawa da kuma karfafa su.
Ga hotunar hidimar.
Kalla: bidiyon shirgar Shugaba Muhammadu Buhari a Borno da Yobe
Samu karin labaran Najeriya a Naija News Hausa