Labaran Najeriya
Mulkin Obasanjo ya fi muni da mulkin Buhari – Balarabe Musa
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna na da, Balarabe Musa ya bayyana a ranar Lahadi da ta gabata da cewa “Obasanjo ya fi muni wajen amfani da cin zari da muzuntawa lokacin da yake mulki bisa ga shugabancin Muhammadu Buhari a yanzun nan”.
Ya ce “Obasanjo yafi rashin tausayi da cin mutunci lokacin da yake a mulki bisa ga yadda ake tunanin Muhammadu Buhari ya ke, Ya kan yi amfani da Iko wajen amfani karfi da ayukan jihohi don muzuntawa dan adawan sa duka”.
“Ba kuwa kawai cin mutunci kawai ba, harma da kashe su” in ji shi.
Wannan shi ne fadin tsohon Gwamnan, a yayin da ake bukatar shi da magana a kan waya.
“Na kula da Obasanjo tun lokacin da ya sauka daga shugabancin lokacin mulkin sojoji’s. Ya kan so ya yi amfani ra’ayinsa dun jagorancin shugaban kasar” in ji shi.
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi barazana, ya ce “Ban yi zaton zan fadi ga zaben 2019 da ke gabatowa ba”
Ganin irin yabawa da goyon baya da kuma irin amincewa da jama’a suka nuna mana wajen yawon yakin neman zabe a yankunan kasar, “Zai zama da mamaki inji cewa na fadi zaben 2019” in ji Shugaba Muhammadu Buhari.
Balarabe ya kara da cewa ba za’a iya bada gaskiya ko tabbaci ga Jam’iyyar PDP ba, haka kuma ba za a bada tabbaci ga Jam’iyyar APC ba, duk kanwar Jaa ce. Ba mai tabbacin shugabanci ta kwarai cikin su. Shi ya sa Obasanjo ke amfani da wadannan zarafi don juya kasar yadda ya gadama.
Ya bayyana da cewa Obasanjo zargin banza da tsince-tsince banza ne kawai ya ke yi game da shugabancin Buhari, don shi ma yayi fiye da hakan.
“Zargin Muhammadu Buhari bai dace a bakin Obasanjo ba, kanwar duk jaa ce” in ji shi.
Ku tuna da cewa tattalin arzikin Jihar Legas na kulle a hannun Obasanjo shekaru da daman sai har da ya sauka shi ne marigayi Yaradua ya bayar da kudaden ga Jihar Legas.
Karanta Kuma: Jam’iyyar APC sun ce “barawo, a ko yaushe barawo ne”, a yayin da suka samu labarin cewa Atiku ya samu shiga kasar Amurka..