Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari ba zai raba tattalin Arzikin Kasa ga ‘Yan uwa, ko ga Abokannai ba – Osibanjo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osibanjo ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari ba zai rarraba arizikin kasar ga ‘yan uwansa ko kuma ga abokansa ba.

Osibanjo ya ce “Shugaba Buhari ya dace da kara komawa ga mulki saboda irin gwagwarmaya da kokarin sa wajen yaki da babban matsala ta musanman da ke ci mana tuwo a kwarya kasar, watau Cin Hanci da Rashawa”.

“Cin hanci da rashawa wani babban cuta ne da ya rigaya ya cinye tattalin arzikin kasar Najeriya, ya raunana arzikin kasar da gaske tun shekarun baya a hannun shuganan da suka jagoranci kasar” in ji Osibanjo.

Ya kwatanta ayukan da gwamnatin da suka fara da basu kare ba a matsayin halin cin hancin ne da rashawa.

Farfesa Osibanjo ya bada tabbaci ga ‘yan Najeriya a wata ganawa da yayi da Matasan Addinin Krista a Jihar Legas a shiyar Ikeja, inda ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari ba zai rarraba tattalin arzikin kasar ga ‘yan uwa ko ga abokan sa ba” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito ‘yan kwanaki da suka wuce da cewa dan takaran shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gabatar da shirin sa idan har ya ci zaben shugaban kasar Najeriya.

Atiku ya kara da cewa wani abin mahimi da zai yi kuma shine tabbatar da cewa abokannan sa sun yi arziki sosai.

Farfesa Osibanjo ya kara da cewa “Mutanen da suka lalace tattalin arzikin kasar ke ikirarin cewa za su zo su gyara kasar. Ya kamata mu tambaye su yada zasu iya hakan, Ko dai zasu zo ne su watsar da arzikin kasar ga abokanan su? ya kamata mu bincike su akan haka”

Mataimakin shugaban kasar ya karshe da cewa ya bukaci hadin kai da jimrewa daga Kiristoci da Musulunman Kasar don kai ga cin nasara da kuma samun zaman lafiya a kasar.

Kalla: