Connect with us

Uncategorized

Ba zamu raunana Amincin mu ba – INEC

Published

on

at

advertisement

Shugaban Hukumar kadamar da Zaben Kasan Najeriya (INEC), Mahmoud Yakubu ya fada da cewa hukumar ba zata juyewa amincin da take da shi da don wata tsanani ko damuwa.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Hukumar Kadamar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta bayyana matakai bakwai da za a bi wajen jefa kuri’u a ranar zabe ta 2019 kwanaki da suka gabata.

Duk da hakan Tsohon shugaban kasan Najeriya ya zargi hukumar da cewa suna da shirin yin makirci ga zabe na gaba ganin irin halin tsanani da gudanarwa da hukumar ke ciki da kuma irin alamun gani da cewa hukumar za ta aiwata makirci don taimaka wa Jam’iyyar APC da cin zaben. Jin hakan shugaban hukumar INEC ya mayar da martani da cewa “Ba za mu zubar da mutuncin mu ba don wata tsanani ko damuwa a kasar” in ji Mahmoud.

Mun sami sani a Naija News da cewa shugaban hukumar INEC ya yi ganawa da Babban shugaban jami’an tsaron ‘yan Sandan kasar, Mohammed Adamu a ranar Litini da ta gabata a babban birnin tarayya, Abuja inda Mahmoud ya bayyana kalaman.

Ya ce “Hukumar mu ba ta cikin wata tsanani da har zai sa mu zubar da mutuncin mu ko aiwatar da abin da bai kamata ba”

Ya kara da cewa “bai yi mamaki ba da fade-faden mutane akan hakan, cewa duk lokaci irin wannan da zabe ya kusanto, mutane zasu yi ta maganganu iri tasu” in ji shi.

Ka tuna; Hukumar INEC ta mayar da martani a baya ga jam’iyyar PDP a kan zaɓan Amina Zakari a matsayin mai kula da karban zabuna. INEC sun ce wa Jam’iyyar PDP “Ba za ku koya mana aikinmu ba”

Shugaban INEC, Mahmoud a cikin bayanan sa ya bada tabbacin zaben ta kwarai ga ‘yan Najeriya.

“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya da cewa kuri’un su ne kawai ba wata abu ne zai zamana ba ga zabe ta gaba” in ji shi.

“Da irin hadin gwuiwa da hukumomin tsaron kasar suka bayar da kuma su ke shirin aiwatar, ‘lallai ina tabbatar maku da cewa zamu aiwatar da zaben shekara ta 2019 a hanyar da ta dace” in ji Mahmoud.