Connect with us

Uncategorized

John Hayab, Kakakin Kiristocin Jihohin Arewa 19 ya ki matsayin da PDP suka nada shi

 

Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa Rev. John Hayab, Kakakin yada yawun Kiristoci Najeriya ta Jihohin Arewacin kasar guda 19 ya ki matsayin da Jam’iyyar PDP suka sanya shi a ranar Asabar da ta gabata.

Jam’iyyar sun nada John ne a matsayin babban mai jagorantar hidimar yakin neman zabe ta Jam’iyyar PDP anan Jihar Kaduna ga zaben ta gaba.

Kakakin Jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Abraham Catoh ne ya bada tabbacin hakan ga manema labaran Premium a ranar Asabar da ta gabata da maraice.

Ko da shike an bayar da cewa Re. John Hayab ya ki wannan matsayi da Jam’iyyar ta nada shi.

Akwai sani da cewa ba a dade ba da aka sanya Rev. John Hayab a matsayin ciyaman na Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a nan Jihar Kaduna.

Bayan wannan ne Jam’iyyar PDP suka duba da cewa ya dace su kara wa irin wannan mutumin matsayi da girma amma abin mamaki, Hayab ya ki hakan.

Ya gaya wa manema labarai da cewa lalai da gaske ne aka nada shi ga wannan matsayin amma dole ne ya ki wannan matsayin saboda, ba a dade ba Kungiyar Hadaddiyar Kiristocin Jihar suka sanya shi matsayin Kakakin kungiyar.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana da cewa “kowaye ya sanya a matsayin abokin dan takaransa a Jihar, ko da ma Paparoma ne, Kiristocin Jihar ba za su zabe shi ba” in ji El-Rufai.

John Hayab ya ce “don a sanar da zabi na a matsayi bai zama da dole wai sai na yadda da hakan ba”, ko da shike na san da cewa Jam’iyyar PDP sun sanya ni ne a wannan matsayi don sun ga ya dace da hakan.

Ya kara da cewa “Na tuna da cewa Shugaban Kulawa da jagorantar Jarabawan ‘yan shirin shiga Jami’a (JAMB), watau Mista Ishaq Oloyode shugaba ne harwa yau na Kungiyar Zamantakewar Musulunman Kasar Najeriya”

“Kawai bukata ta shi ne ci gaban Jihar Kaduna da al’ummar ta gaba daya” in ji Hayab.

 

Karanta kuma: Mulkin Obasanjo ya fi muni da mulkin Buhari – inji tsohon Gwamnar Jihar Kaduna, Balarabe Musa

Advertisement
close button