Connect with us

Uncategorized

PDP: Atiku Abubakar zai ziyarci Jihar Imo yau don hidimar neman zabe

 

Dan takarar Shugaban Kasar Najeriya daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da magoya bayansa za su ziyarci Owerri, Jihar Imo a ranar yau 22 ga watan Janairu, 2019 da za a yi a filin wasan kwallon kafar Sam Okpara nan yankin Owerri.

Dan takaran da ya bukaci ‘yan Najeriya su gafarta masa da matakin da ya dauka na kauracewa zaman muhawarar dan takaran shugaban kasa da aka yi Asabar da ta gabata kamar yadda Naija News Hausa ke da sanin wannan, ya aika a yau a shafin nishadin sa na twitter da cewa zasu ziyarci Jihar Imo don gudanar da na su hidimar neman zaben a Jihar.

Naija News ta ruwaito da cewa a ranar jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Borno da Yobe inda muka sami labarai da cewa mutane cin cika filayen makir don marabtan shugaba. Harma da baya mun samu rahoto da cewa akwai wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar hawar kan gini don ganin shugaban, da kuma wadanda suka ji raunuka sanadiyar takewa da aka masu wajen leke-leke.

Alhaji Atiku ya bukaci ‘yan Jam’iyyar da magoya bayansu da fitowa don wannan hidimar da za su yi a yau.

Sakon na shi na kamar haka a shafin twiter;

Bayan Shugaba Atiku ya yi wannan kirar, wasu magoya bayan shi da Jam’iyyar sun nuna farin cikin su da wannan kuma sun bayyana da cewa suna a shirye don hidimar.

Ka fadin kamar haka:

 

Advertisement
close button