Connect with us

Labaran Najeriya

Siyasa: Obasanjo da Buhari sunyi ganuwa a yau bayan mayar da martani zargi ga juna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun yi ganawa da juna a yau a birnin Abuja a wata taron ganawa ta hukumomin kasar, bayan martanin zargi da shugabanai biyun ke ta aika wa juna akan shugabancin kasan nan.

Muna da sani a Naija News da cewa Obasanjo ya gabatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai da lafiyar jiki da lafiyar ruhu a wata bayanin shi ga manema labaran BBC a ranar Litini da ta gabata. Harma da baya ya kara da cewa shugaban ya je ya huta ya bar ma wani jagorancin kasar nan.

Obasanjo ya bayyar a wata gabatarwan shi inda ya kwatanta shugabanci da jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da irin ta Marigayi tsohon shugaban Sani Abacha a Najeriya. “Kada ku yarda Buhari ya kara yaudaran ku karo na biyu” in ji Obasanjo.

Ko da shike Buhari bai dauki wannan da wasa ba, shi ma ya mayar da yawu akan batun, yayin da ya ce “Obasanjo na bukar kulawar dakta don samun cikakken lafiyar jiki” inji fadin Buhari ta bakin kakakin yada sawun sa, Garba Shehu.

Duk da wadannan maganganu da martani daga shugabannan, sun gana yau  harma sun gaisa da juna a wajen taron.

Taron ya halarcin shugabai kamar, Tsohon shugaban kasa Ernest Shonekan, Abdulsalami Abubakar, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Babban shugaban sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki, Shugaban kasa na da, Goodluck Ebele Jonathan hade da wasu Gwamnonin Jihohin kasar.

Rahoton taron zai biyo daga baya….

Ga hotunan taron:

 

Karanta kuma: Atiku Abubakar zai ziyarci Jihar Imo yau don hidimar neman zabe