Connect with us

Labaran Najeriya

Atiku yafi Buhari kirki ko ta yaya – in ji Obasanjo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana a wata ganuwa da manema labaran BBC da cewa dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai fi Buhari taka rawar gani a mulki mai kyau  har so biyu.

“Kowane na iya satar tattalin arzikin kasan nan kuma ya tsira idan har dan Jam’iyyar APC ne shi” in ji Obasanjo.

Ya ce, shugaba Muhammadu Buhari ya nuna kasawar shi ga iya mulkin kasar Najeriya cikin ‘yan shekaru da ya hau mulki.

“Lallai Atiku ba Almasihu ba ne, kuma ba fitacce ba ne a gaskiya, ya kasa da baya kuma ya zo don nemar gafara ga kasawar sa da kuma gyara abin da ya lalace” in ji Obasanjo.

“Ni Kirista ne kuma mai bangaskiya, kuma koyaswar addini na ya bayyana mani da cewa dole ne ka gafarta ma wadanda suka aikata maka Iaifi idan har kaima kana son a gafarta maka laifunan ka, ba kada wani dalilin rokon gafara ga Allah idan har kaima ka ki ka gafarta ma wadanda suka yi maka laifi” in ji tsohon Shugaban.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Obasanjo ya kwatanta shugabancin Muhammadu Buhari da shugabancin marigayi tsohon shugaban Najeriya, watau Sani Abacha.

“Ni mai zunubi ne, ina kuwa son Allah ya gafarta mani zunubai na, ya kuwa zama dole in gafarta ma wadanda suka aikata mani laifi”

“A halin yanzun nan dan takara babba guda biyu ne kawai muke da su ga zaben 2019, Buhari daga Jam’iyyar APC da kuma Atiku daga Jam’iyyar PDP. A nawa sanin, Buhari ya nuna kasawar shi ga mulkin kasar, ya nuna halin cin hancin da rashawa, mugunta, sonkai, da rashin amana a shugabancin shi.

“Buhari ya kasa ga hankali da kuma karfin jiki, Ni kuwa na bada gaskiya cewa Atiku zai fi iya jagorancin kasar bisa Buhari har ma ya ninka shi sau biyu” in ji shi.

 

Karanta kuma: Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a birnin Abuja wajen zaman tattaunawar jigon jihohi