Connect with us

Uncategorized

Ba mu amince da 27,000 a matsayin kankanin albashin Ma’aikatar kasa – NUT

 

Bayan matakin da Majalisar Dokoki ta Jiha da shugabancin kasa ta yi a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, na amincewa da biyar kankanin albashi na naira dubu 27,000 kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa, sakamakon tattaunawa da shugabannan kasar suka yi a birnin Abuja ranar Jiya.

‘Yan Kungiyar Mallamai Tarayya ta Kasar Najeriya (NUT) sun tada barazana da cewa basu amince da wannan matakin ba.

Ko da shike Shugaban Hukumar Ma’aikata ta Kasa, Mista Chris Ngige ya kauracewa gwamnatin tarayya akan wannan batu na biyar dubu 27,000, da cewa dole ne gwamnatin tarayya ta cika naira dubu ukku 3,000 da ya saura daga dubu 30,000 kamar yadda suka aje arjejeniya da baya.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Kungiyar Ma’aikatan Kasa sun yi ganawa a kwanakin baya inda suka tattauna akan shirin sabon albashin, har suka yi barazanar cewa zasu ci gaba da yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya dace ba ga kungiyar.

Sakataren Kuniyar NUT, Dokta Mike Ene ya bayyana ga manema labaran Najeriya a birnin Abuja a yau da cewa Majalisar Dokokin Kasa su yi kokarin samar da biyan wannan kankanin albashin ma’aikata ga dukan yankuna, kada ya kasance ga wasu yankuna kawai.

Ya ce “Ma ‘aikaci, ko ina ma’aikaci ne, ba wai kawai sai wanda ke aiki da gwamnatin tarayya ne kawai za a yi wa karin albashin ba, amma har da wadanda ke aiki tare da jihohin a karamar hukumomi. saboda hakan, ayi kokarin magance wannan banbancin na cewa ga ma’aikatan tarayya ne kawai za a yi wa karin albashin” in ji shi.

Advertisement
close button