Uncategorized
IDP: Alinko Dangote ya bada tallafin abinci ga mutane 30,000 a Jihar Zamfara
Sanannen Maikudin Afrika, Alhaji Alinko Dangote ya bada tallafin abinci da kimanin lisafin kudi na miliyan da yawa ga wadanda aka wa hari da barna a Jihar Zamfara sakamakon hare-haren da mahara suka kai wa Jihar.
Kamar yadda lissafi ta bayar, kimanin yawan mutane 3,000 ne suka rasa rayukan su sakamakon hari a Jihar Zamfara, fiye da mutane dari biyar 500 ne aka sace, kuma kusan mutane 100,000 sun yi gudun hijira, haka kuwa kimanin mutane 30,000 na a hade inda Gwamnati ke nuna masu kulawa a yankin Maradun da ke a Jihar.
Babban maikudin ya kafa wannan shiri ta musanman don taimakawa rayukan da suka saura a Jihar ta wurin basu abinci isasshe da kayan rayuwa don samun karin jiki.
Mansur Ahmed, shugaban Harkokin Kasuwanci da Gwamnati ne ya mika wadannan kayan abinci ga mutanen a wakilcin shugaban Kamfanin, watau Alhaji Aliko Dangote.
Ya ce “Alhaji Dangote ya nuna bakin ciki game da wadanda suka yi gudun hijira don ceton ransu, kuma yana fatan za a dauki mataki ta musanman ga wannan abin” in ji shi.
Ya kara da cewa Kamfanin Dangote na shirin kafa wata gidan tsarrafa shinkafa, kuma idan har an kallama shirin a wanan shekara, za a sanya dubban mutane daga nan Jihar Zamfara don samun aikin yi.
Sarkin yankin Maradun, Muhammad Garba Tambari ya ce “Ina da murna mara matuka da wannan babban shiri da Kamfanin nan ta yi a garemu a wannan yankin ta wurin taimakawa da kayan abinci, Kamfanin Dangote ne farkon yin hakan, kuma mun gode da gaske da wannan taimakon” in ji shi.
Kayakin abinci da aka bayar na kamar haka:
Lodin Tirela da Alkama
Lodin Tirela da Spageti
Lodin Tirela na Siga
Lodin Tirela na garin tuwon Semo
Lodin Tirela na Makaroni da sauran kaya da ba ambata ba.
Jama’ar Marudun sun nuna farin cikin su da wannan babban shirin, sun kuwa godewa Kamfanin Dangote kuma a karshe sun bayyana da cewa abin takaici ne irin mugayen hari da ake kaiwa ga Jihar.
Sun kuwa yi kira ga Gwamnatin don magance wannan hare-haren da cewa kusan shekaru biyar yan zun nan, jihar ba ta kasance da zaman lafiya ba.