Najeriya na cikin Tallauci sanadiyar Buhari da Jam’iyyar APC- inji Atiku

Alhaji Atiku Abubakar, Dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP ya bayyana da cewa Buhari ne da Jam’iyyar APC ke tallautar da kasannan.

Ya ce, Kasar Najeriya da aka sani duk Afrika da kuma duk kasar duniya da cewa tana da Isasshe kayan fahariyya da Isasshen tattalin arziki. Harma akan yi ikirarin da cewa “Najeriya babbar Jigon Afrika, kasa mai zuba da madara, amma yanzun nan an sanya mu cikin layin kasa mai mumunar talaucewa a tarihi”.

Atiku ya bayyana wannan ne wajen ziyarar sa a birnin Owerri inda ya je yakin neman zabe kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da cewa Atiku Abubakar da ‘yan Jam’iyyar PDP sun ziyarci Jihar Imo don  kadamar da yawon yakin neman zabe a jiya Talata, 22 ga watan Janairu, 2019.

“Buhari da gwamnatin sa na inganta tallauci da lalacewar tattalin arzikin kasar nan” in ji Atiku.

Dan takaran Gwamnan Jihar Imo daga Jam’iyyar PDP, Emeka Ihedioha ya kara da rokon ‘yan kungiyar Iyamirai duka da su goyi bayan Atiku da Jam’iyyar PDP don cin nasara ga zaben karon nan.

“Jam’iyyar APC ta kasa ga shugabanci, wannan lokaci ne da kungiyar Iyamirai za ta tashi don goyawa Atiku da Jam’iyyar PDP baya ga samun ci gaban kasar mu” in ji shi Emeka.

Atiku ya karasa da cewa, kasar mu na cikin tallauci, rashin tsaro, ba aiki ga jama’ar kasa, komai ya lallace, “Jam’iyyar APC ba ta da wata manufa da shirin kwarai ta gyara kasar nan, sun yaudari al’ummar kasar nan, bai kamata mu basu dama ba don sake yaudaran mu”.

“Ina kira gareku duka jama’ar Imo ku fito ku jefa mani kuri’ar ku, kuma ku kasa ku tsare kuri’ar don muna a sane da cewa Jam’iyyar APC na shirin Makirci ga zaben, kuma ba zamu bada damar hakan ba” in ji shi.

Ya ce “Za mu samar da shugabancin da zai bawa kowa murya a kasar nan, samar  da ayuka, harma da karfafa Jihohin don bunkasa tattalin arzikin kasar”

Atiku ya aika a shafin nishadin twitter na shi kamar haka bayan dawowar sa daka ziyarar;

Duk da hakan an sami wasu da suka bayyana ra’ayin su ga zaben kamar haka; a turance:

https://twitter.com/Victoria_NGR/status/1087763361805336576

Ku tuna da cewa Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fada da cewa “Ko da shike Atiku ba Almasihu ba ne, amma ya fi Buhari kirki har sau biyu” Wannan shi ne fadin tsohon shugaban a wata bayanin sa da manema labaran BBC kwana biyu da suka wuce.

 

Karanta kuma: Mulkin Obasanjo ya fi muni da mulkin Buhari – Balarabe Musa