Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 24, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 24 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Zan biya ma’aikata kankanin albashi na 100,000 idan aka zaɓe ni – Sowore

Dan takarar shugaban kasa Najeriya na Jam’iyyar (AAC), Mista Omoyele Sowore ya yi alqawari da cewa, idan har aka jefa masa kuri’a kuma ya ci zaben shugaban kasa ta gaba, zai biya ma’aikata 100,000 a matsayin albashi mafi kankanci.

Dan takaran ya yi wannan alkawarin ne a wata ganuwa da suka yi da manema labaran NTA da DARIA a birnin Tarayya, Abuja.

2. Dalilin da ya sa bamu Karawa Shugaba Buhari ba – Bukola Saraki

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da shirin ta na rinjayar Shugaba Muhammadu Buhari a kan dokar zaɓen da ya ki kadamarwa saboda rashin samun mutanen da daman da suka sanya hannu ga yin hakan, in ji Sanata Bukola Saraki.

Sanatan ya gabatara da wannan ne a ranar Laraba da ta wuce ga manema labaran wata gidan telebijin.

3. ‘Yan sanda sun yi watsi da zargin cewa sun kame Rotimi Amaechi a filin jirgin saman Port Harcourt

Rundunar Jami’an tsaron ‘Yan Sanda da ke a Jihar Rivers sun karyace zancen da ake yi da jam’iyan na cewa sun kama tsohon gwamnan jihar da ministan harkokin sufuri, Mista Rotimi Amaechi.

Ofisan Yada Labarai na Jami’un, (PPRO) Nnamdi Omoni ya yi gabatarwa a yayin da ya wakilci Kwamishanan Jami’an Jihar, Usman Belel da cewa duk fade-faden karya ne da kuma shirin masu makirci.

4. Oby Ezekwesili ta janye daga tseren takarar shugaban kasa ta shekarar 2019

‘Yar takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Allied Congress (ACPN), Oby Ezekwesili ta janye daga tseren zaben shugaban kasa da za a  yi a ranar 16 ga Watan  Fabrairu.

Mun sami tabbacin hakan a Naija News da cewar ‘yar takaran ta yi hakan ne yau da safen Alhamis 24 ga watan Janaiiru, da cewa wannan matakin nata tayi shi ne don taimakawa wajen cin nasara ga Jam’iyar APC da Jam’iyyar PDP.

5. Bayanin banza ce na cewar Atiku ya samu shiga Amurka ne a matsayin ma’aikaci na – Saraki

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya ce “dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bai tafi Amurka ba a matsayin mataimaki na”.

A yayin da ya ke bayani da wata gidan talabijin a ranar Laraba, Saraki ya ce “Zancen banza ce da cewa Alhaji Atiku Abubakar ya bi ni zuwa kasar Amurka ne a matsayin mataimaki na”. in ji shi.

6. Nnamdi Kanu ya bayyana yadda Atiku ya bada tabbacin cewa Buhari ‘Jubril’ ne

Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya yi zargin cewa Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya bada karin tabbaci na cewar Shugaba Muhammadu Buhari ‘Jubril’ ne da ake batu.

Ya ce, a gabatarwar Atiku a ranar Talata da ta wuce, ya bayyana da cewa lallai Buhari bai jin yaren Fulfude (Fulani). Wannan shi ne tabbacin shi na cewar a musanya shugaba Muhamamdu Buhari da ‘Jubril’.

7. Kotun Koli ta Tarayya ta sake tsarafa Alkalan ta

Matakin tsarafa alƙalai da kotun koli ta birnin tarayyar ta gudanar ya mayar da Alkali Okon Abang zuwa Abuja, Alkalin da daman aka kaishi birnin Asaba shekaru biyu da suka gabata ya dawo Birnin Abuja.

Wannan matakin ya abku ne a yayin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙari ta tsige babban Alkalin Shari’ar kasar Najeriya, Walter Onnoghen akan rashin bada kasafin kudi da ya dace kamar yadda doka ta bayar.

8. Sojojin sun ce karya ne da zargin da ake yi, Babu tashin hankali a Jihar Delta

Rundunar sojojin Najeriya sun mayar da martani game da fade-faden da ake yi da cewar akwai tashin hankali a Jihar.

“Wannan karya ce da kulle-kullen makirci daga wasu don tayar da hankalin jama’a.

9. Nine na fara bayanna makircin babban Alkali CJN Onnoghen – in ji Sowore

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar (AAC), Omoyele Sowore ya ce shi ne mutumin da ya fara gabatar da makirci da halin rashin gaskiyar Babban Alkalin Shari’ar Najeriya, (CJN) Walter Onnoghen wanda ke da asusun kudi da ba a san da su ba.

Dan takaran ya bayyana wannan ne a ranar Laraba da ta wuce a wata ganawa da abokin takaran sa na Jam’iyyar ACC, Dokta Rabiu Rufai ya halarta.

10. ‘Yan Ta’addan Boko Haram sun kai hari a garin Geidam dake jihar Yobe

‘Yan Boko Haram sun kai farmaki a garin Geidam, ta Jihar Yobe da harbe-harbe ga mazaunan birnin.

A bayanin mazaunan wajen, ‘yan ta’addar sun yi amfani da kasuwa ne don gurfanar da wannan mugun harin.

‘Yan ta’addan sun fado wa garin ne da farmaki misalin karfe 5:30 na maraice a inda suka shigo da harbe-harbe ga iska.

 

Ka sami karin labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa