Connect with us

Uncategorized

‘Yan Najeriya sun Mamaye Birnin Abuja da zargin Obasanjo da halin Makirci da Kulle-kulle

 

A ranar Laraba da ta gabata, ‘Yan Najeriya sun mamaye birnin Abuja da zanga-zanga da ikirarin cewa gwamnatin ta kame tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo.

Sun ce “Obasanjo tsohon banza ne, a kame shi, ya janye kansa da lamarin shugabancin kasar”.

“Obasanjo bai nuna kanshi kamar babba ba, da irin kalaman da ya ke furdawa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari”

Wasu Manyan ‘yan siyasar kasan su rattaba baki ga maganan.

Maganganun na kamar haka: A shafin nishadin twitter

Kalli Bidiyon yadda ‘Yan Najeriya suka nuna bacin ran su da bayyanin tsohon shugaban

Tsohon Shugaba, Olusegun Obasanjo ya fada a wata ganawa da cewa “Atiku ya ninka Buhari sau biyu ga halin kirki”

Haka kuma kwanakin baya ya ce, Buhari ya kasa da lafiyar jiki da kuma ruhu.

“Mutun na iya sace kasar Najeriya dungun ba tare da an kame shi ba, idan har dan Jam’iyyar APC ne shi” in ji Obasanjo.

“Ka sauka ka ba wani damar jagorancin kasar Najeriya” in ji fadin Obasanjo a wata bayyanin da ya yi da aka watsar a layin yanar gizo.

Wadannan kalaman ne ya bata wa ‘yan Najeriya rai da har suka zabura da zanga-zanga zuwa birnin Abuja.

Kalli bidiyon inda Obasanjo ya fadi wadannan kallaman:

https://twitter.com/bbcnewspidgin/status/1087394985006252032

Ka sami karin labaran siyasa ta Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button