Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Ina a shirye don mara wa Sowore baya da kujerar takara na – Fela Durotoye

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar (ANN), Mista Fela Durotoye ya gabatar da farin cikin shi game da matakin da ‘yar takarar kujerar shugaban kasa na Jam’iyar (ACPN), Malama Oby Ezekwesili ta dauka na janyewa daga tseren takaran shugaban kasar Najeriya.

Mun sanar a Naija News Hausa da safen nan ta Manyan Labarun Jaridun Najeriya da cewa Malama Oby Ezekwesili da ke tseren kujerar shugabancin kasar Najeriya daga Jam’iyyar ACPN ta janye wa tseren. Ta fada da cewa “Na dauki wannan matakin ne don taimakawa wajen ganin cewa an ci nasara da Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP wajen zaben 2019” in ji ta.

Mista Durotoye  yace “Na yabawa Ezekwesili da irin wannan yanke shawarar da tayi”.

“Ina a shirye don marawa dan uwa Omoyele Sowore da Farfesa Kingsley Moghalu baya wajen ganin cewa an ci nasara ga wannan zaben shugaban kasa ta shekarar 2019″ in ji Durotoye a wata bayyani da ya rattaba hannu a yau Alhamis 24 ga Watan Janairu, 2019.

“Na bada gaskiya da cewa shugabanci ta kumshi sadaukarwa ne, haka kuwa yau ina jinjina wa Dokta Oby Ezekwesili ga sadaukarwa da ta yi na nuna halin shugabanci ta wurin janye wa tseren don marawa wani baya ga cin nasara ga zabe ta gaba” in ji shi.

“Idan har za a hada gwuiwa a ajiye dan takara guda ga zaben nan, Lallai ni da kaina ina shirye don mara masa baya da duk karfi da abin da na tara wajen ganin cewa an sami nasara ga zaben 2019 da ke gaba”

“Bari mu hada kai da gwuiwa don daukar wannan dama ta cin ma gurin mu na ganin cewa kasar nan ta ci gaba, mu sanya mutum daya gaba don wakilcin mu, mu kuwa mu biyo daga baya don ci gaban kasa, da kuma samar da murya daya ga zaben tarayya da ke gaba”

“Al’umma sun zuba mana ido da ganin irin rawar da zamu taka, ba zai zama da kyau ba ace mun kunyata su” in ji Durotoye.

 

Karanta kuma: Kakakin Kiristocin Jihohin Arewar  Najeriya 19, John Hayab ya yi murabus da matsayin da Jam’iyyar PDP suka nada shi