Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Lokaci ya kure miki da janye wa tseren takara – INEC ta gayawa Ezekwesili

 

Hukumar gudanar da zabe, INEC ta ce bata amince da janyewar ‘yar takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar ACPN, Dokta Obiageli Ezekwesili ba.

Mun sanar a Naija News Hausa da safen nan da cewa, Dokta Obiageli Ezekwesili, ‘yar takarar shugaban kasa ta janye daga tseren da cewa tayi hakan ne don taimakawa wajen magance gwagwarmaya da ke tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

Hukumar INEC sun mayar da martani a kan wannan matakin, da cewa lokaci ya kure da daukar irin wannan matakin.

A yau Alhamis a nan birnin Abuja, Sakataren Hukumar INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya gabatar da cewa basu amince da matakin ba, da cewa lokaci ya rigaya ya kure na daukar irin wannan matakin.

“Bai yiwuwa wani dan takaran shugaban kasa ya ce zai janye a wannan lokaci” inji Mista Rotimi.

“Kamar yadda sharidu da dokar hukumar ta bayar kan zaben 2019, ranar 17 ga watan Nuwamba, 2018 ne aka bayar a matsayin ranar karshe da duk wani dan takara zai iya janye wa tseren” in ji shi.

Ko da shi ke, da safen nan mun ruwaito da cewa, Dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar (ANN), Mista Fela Durotoye ya gabatar da farin cikin shi game da matakin da ‘yar takarar kujerar shugaban kasa na Jam’iyar (ACPN), Obiageli Ezekwesili ta dauka na janyewa tseren takaran shugaban kasar Najeriya.

 

Karanta wannan kuma: Mutane biyu sun mutu a Jihar Sokoto wajen Rallin Shugaban Kasa

Advertisement
close button