Connect with us

Labaran Nishadi

Boko Haram: Ga wata bidiyo inda Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram ke tura Motar yaki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Duk da irin zafin hari da ‘yan ta’ddan Boko Haram ke aikawa rundunar sojojin Najeriya da Jihohin kasar, na gano wata bidiyo inda motar yakin rundunar sojojin ya lake a hanya har suna tura motar da karfin su don sake tada motar.

Wannan bidiyon ya bi ko ta ina a yanar gizo, harma wasu na zargin shugabancin kasar da cewa bai dace ace rundunar sojojin kasar da ke yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram su rasa isasshen kayan yaki ba.

“Ganin sojojin na tura motar yakin bai da ce ba da kasar mu”.

Duk da cewa rundunar sojojin sun yi kira a kwanakin baya da cewa makaman yaki ya kasa masu, sai gashi suna tura motar yaki da ya lallace.

“Yawancin motocin da muke amfani da su, sun lallace” in ji sojojin.

Kalli bidiyon

Wani sanannen dan Najeriya ya aika bidiyon a shafin nishadin shi, inda ya bayyana shugabancin Najeriya sun sadaukar da ran sojojin kasar ga ‘yan ta’addan Boko Haram da barin su da irin wanna mataccen motar yaki.

Sakon na kamar haka: