Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari bai iya mulkin kasar nan – in ji PDP

Published

on

at

advertisement

Jam’iyyarn PDP sun zargi shugaba Muhammadu Buhari da kasawa ga iya mulkin kasar Najeriya

A hidimar yakin neman zabe da Jam’iyyar PDP ta yi a Filin Kwallon Ahmadu Bello da ke a Jihar Kaduna, a ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Jam’iyyar PDP na Tarayya, Uche Secondus ya ce “Buhari raggage ne, ba zai iya jagorancin kasar nan ba” inji Uche.

“Buhari ya yi iyakar kokarin sa, ya koma kauyen su ya huta” in ji shi.

“Ba ma son shugaban da zai bar wata rukuni na daukar gurbin sa a shugabanci. Lokaci yayi da zamu gayawa shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya je ha huta, ya rigaya ya taka irin nasa rawar gani, ya koma gida yaje ya huta gajiya saboda bai saura da wata karfin jiki ba, ya zama raggage”

“Muna bukatar shugaban da zai iya aiki da tsawon lokatai, ba shugaba mai barci ba, ba shugaba marasa lafiyar jiki irin tashi ba, muna bukatar mutum mai karfin jiki sosai da gaske, mutumin da zai iya gudanar da aiki ba tare da barin wata rukuni na jagoranci ba” in ji Uche.

Ya ce, Idan har mun bar shugaba Buhari ya cigaba da mulki a kasar nan, lallai, za a karu da yunwa, rashin tsaron kasa da sauran su, ganin irin yadda suke barci ga mulki.

“Lokaci yayi da zamu fada wa shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya koma gida ya huta”.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyar PDP a baya sun shawarci shugaba Buhari da komawa gidan sa a Daura ya huta. sun fadi wannan ne wurin amsa wa rokon Shugaban inda yace  ‘yan Najeriya su bashi lokaci kadan don kadamar da nufinsa ga kasar.

Haka kuwa ‘yan Najeriya makon da ta wuce suka ce shugaban ya kasa da karfin jiki, ganin irin faduwa da yayi a wajen yakin neman sake zabe da aka gudanar a Jihar Delta. Sun ce “Shugaba Muhammadu Buhari ya tsufa, kuma bai da cikaken lafiyar jiki da har zai kara shugabancin kasar nan”.

Shugaban Jam’iyyar PDP na tarayya ya kara da cewa “Ba wanda zai kara yin makirci ga zaben kasar nan”.

Uche ya shawarci Hukumar gudanar da zabe da cewa su guje wa batun nuna makirci ga zabe ta gaba.

Dan takaran shugaban kasar na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kara da cewa, zamu magance rashin tsaro a kasar nan, kuma zamu mayar da kasar nan harma fiye da yadda tattalin arzikin kasar take a da.

Kalla kuma: Ziyarar Atiku Abubakar a Jihar Kaduna wajen yakin neman zabe