Connect with us

Labaran Najeriya

Miji ya bawa Matarsa saki biyu don ta ce za ta zabi Buhari ga zabe na gaba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani mutum ya ba wa matarsa sakin aure har biyu don matar ta bayyana da cewa zata zabi shugaba Muhammadu Buhari ga zaben da ke gaba.

Mallam Abdullahi Yadau ya saki matarsa Hafsat Suleiman don ta bayyana zabin ta ga zaben tarayya da ke gaba.

Mutumin da ke da zama a yankin Kanam, a Jihar Plateau ya saki matar nasa ne akan ta bayyana da cewa zata jefa wa shugaba Muhammadu Buhari kuri’a ga zaben da za a yi a Watan Fabairu da ke gaba.

Tabbacin wannan labarin ya isa ne ga manema labaran BBC kamar yadda maigidan ya bayyana garesu.

“Na sake ta ne a gabar iyayen ta, bayan ta nuna zabin ta ga Shugaba Muhammadu Buhari ga zaben kasa da ke gaba, ni kuwa magoya bayan dan takarar Jam’iyyar PDP ne, watau Alhaji Atiku Abubakar” in ji Yadau.

“Da baya dai, ni da matar nawa mun yi ta jefa wa Muhammadu Buhari kuri’un mu sakamakon so da muke da shi ga shugaban, amma ganin irin kasawar shugaban a jagoranci, na ki shi da gaske yanzun na” in ji shi

“Da matar nawa kuwa ta nuna da cewa harwa yau ta na son shugaban kuma za ta zabe shi, sai na gaya mata da cewa yin hakan na iya raba mu ga aure”

Ku tuna da cewa a kwanakin baya mun sanar a Naija News da cewa matar shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari ta bukaci jama’a su saken zaben mijin ta don kadamar da ayukan da zai kara jawo wa kasar ci gaba.

Yadau ya kara da cewa, rashin arjejeniyar ya kwan biyu tsakani na da ita har ma sai da na kai ga dukarta har ma ga kare mata hakora. Da makwabtan mu suka ji ihun ta, sun shigo gidarmu don gane abin da ke faruwa amma ba wanda ya tanka masu ko kuma bayyana masu abin da ke aukuwa. “Ta bar gidan ne da kanta, ta komawa iyayen ta da ta ga abin ba sauki” in ji shi.

“Ganin hakan Iyayen ta suka aika mini kuma na je da jin kiran saboda ina girmama wa iyayen nata kwarai da gaske. Isa na a gidan kuwa na bayyana masu abin da ya faru duka, kuma na iya nuna masu da cewa ba zamu iya zama tare ba idan har ba zata bi umurni na ba, da na gan cewa bata canza da zabin ta ba har gaban iyayen sai na sake ta da aure” in ji Yadau.

“Ko da shike iyayen nata basu ji dadin hakan ba, ni kan ba zani iya zama da matar da bata bin umurnin mijinta”.

“Ba zamu yadda ‘yar uwarmu ta koma gidan mijin ta ba da irin wannan hali na shi. ko da shike mun dauki matakin dukar mijin tun ba baya, amma tsohon mu ya hana mu da yin hakan” in ji Ibrahim, dan uwar Hafsat.