Connect with us

Uncategorized

Rundunar Operation Lafiya Dole sun ribato makaman yaki a Borno bayan kashe ‘yan ta’adda Hudu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun sami tabbatacen rahoto a Naija News da cewa Rundunar Sojojin Najeriya, Operation Lafiya Dole sun rinjayi ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a yankin Konduga, anan Jihar Borno.

An sanar da cewa Sojojin sun kadamar da zagayen daji don kame ‘yan ta’ddan a wajen buyar su da ke a Makinta Meleri a nan yankin Kodunga inda suka samu kashe ‘yan ta’ddan guda hudu kuma suka ribato makaman aiki da dama a wajen.

Sun ribato makamai kamar su, AK-47 (guda hudu), Bindigogin yaki da lambobin su kamar haka, 58012289, 565240898 da 58006027.

Sun kuma gano wasu mugayen Bindigogi guda uku daban da wanda aka lisafta a sama, kekunar hawa 3, da sauran su dai kamar yadda wani babban shugaban Jami’an tsaron Col. Ado Isa ya sanar mana a Naija News a yau Jumma’a 25 ga watan Janairu, 2019.

Ko da shi ke mun sami gano wata biyo inda aka nuno rundunar sojojin da ke yaki da ‘yan Boko Haram na tura motar yakin su da ta lake a hanya.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa a baya Shugaban kungiyar hadin guiwa da zamantakewa ta addinin Kiristoci, Bishop Sunday Onuoha ya yi gargadin cewa idan har ba magance matsalar tsaro ba a kasar nan, lallai ba mamaki ‘yan ta’addan Boko Haram su fadawa wa sauran Jihohi da ke arewacin kasar, kamar Jihar Bauchi, Taraba, Gombe da Adamawa.

Sunday ya kira ga wannan la’akari ne a yayin da yake gabatarwa a wata taruwar tarayya da aka yi a birnin Abuja a kwanakin baya.