Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari ya sanya dokar ‘Rashin nuna banbanci ga Raggagu’

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga dokar ‘Rashin nuna banbanci ga raggagu’

Shugaban ya bayyana wannan ne ta wata gabatarwa da Mai kulawa da hidimar shugaban kasa ta gidan Majalisar Dattijai, Sanata Ita Enang a ranar Laraba da ta gabata.

Shugaban ya sanya wa dokar wata liki kamar haka ‘Nuna Banbanci ga Raggagu’

Acikin dokar an bayyana da cewa duk wata rukuni da ta aika laifin nuna banbanci ga raggagun mutane, za a ci ta taran kudi naira Miliyan daya (1m), idan kuma mutum daya ne ya aika laifin, za a ci shi tarar kudi naira dubu dari (N100,000).
Dokar ta cigaba da cewa, akwai jarun shekara shidda (6) ga wanda ya kasa ga biyar kudin kamar yadda dokar ta bayar.

“A cikin dokar kuma akwai shiri na kafa gine-gine a gari, irin wanda zai ba raggagu zamantakewa ta kwarai” inji Enang.

“Kamin wata rukuni, ko mutum daya, ko kamfani ta kafa gine-ginen ta, za a binciki tsarin ginin, idan har bai bi kan doka ba, kuma har ginin zai taune hakin raggagu, lallai za a tada irin wannan ginin kuma hade da biyan tara.

Haka kuwa “Duk wata rukunin gwamnati ko mutum da ya bada izinin a kafa gini irin wadda ba kan doka ba, kuma da zai taune hakin raggagu a kasar nan, lallai za a ci shi tarar kudin miliyan daya (1,000,000) ko kuma a jefa mutum a jarun tsawon shekara biyu hade ma da biyan taran kudin” in ji Enang.
Secretary as the head.”